✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun ceto yaro da aka sayar shekaru 3 a Filato

A cewar rundunar, kawun yaron ne ya sayar da shi shekaru uku da suka wuce.

Dakarun Runduna ta 3 ta ‘Operation Safe Haven’ masu wanzar da zaman lafiya a Jihar Filato sun ceto wani yaro ɗan shekara 12 a Ƙaramar hukumar Riyom da ke jihar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Manjo Samson Zhakom ne ya bayyana hakan a hedikwatar rundunar yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a.

A cewar rundunar, kawun yaron ne ya sayar da shi shekaru uku da suka wuce.

Rundunar ta ce, an kuɓutar da yaron ne bayan wani samame da sojoji suka kai a maɓoyar miyagun da ke a Ƙaramar hukumar Riyom.

Da yake bayyana yadda aka kuɓutar da yaron, Manjo Zhakom ya ce “a ranar 22 ga Yuli, 2025, sojoji sun ceto wani yaro ɗan shekara 12 a lokacin da suka kai samame a maɓoyar ‘yan ta’adda a yankin Riyom.

“Bincike ya nuna cewa, kawunsa ne ya siyar da yaron shekaru 3 da suka gabata, amma an miƙa yaron ga Kansila mai wakiltar mazaɓar Zamko na Ƙaramar hukumar Langtang ta Arewa a jihar Filato, wanda ake sa ran zai miƙa yaron ga danginsa,” in ji kakakin.

A wani labarin makamancin haka, rundunar ta ce dakarun sojin sun ƙwato makamai da alburusai a wani samame da suka kai a Ƙaramar hukumar Wase da ke jihar.

Manjo Zhakom ya bayyana cewa, “Bisa ga sahihan bayanan sirri da suka gano, ‘yan bindiga ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 a kan titin Kampani  zuwa  Kombodoro a Ƙaramar hukumar Wase ta Jihar Filato, sojojin sun yi kwanton ɓauna a kan hanyoyin ’yan fashi da ke kusa da unguwar Jeb.