✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe wasu ’yan bindiga a Filato

sojojin sun yi wa ’yan bindigar kwanton ɓauna tare da tuntuɓar su, wanda ya haifar da musayar wuta.

Dakarun runduna ta 3 Division/Operation Safe Haven sun kashe wasu ’yan bindiga biyu tare da ƙwato makamai da alburusai a Jihar Filato.

An samu labarin cewa, an kai harin ne a ranar Laraba, biyo bayan samun bayanan sirri kan shirin da ’yan bindiga suka yi na kai hari a ƙauyen Nteng da ke Ƙaramar hukumar Qua’an Pan.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, mai magana da yawun rundunar soji ta musamman, Manjo Samson Zhakom, ya ce sojojin sun yi wa ’yan bindigar kwanton ɓauna tare da tuntuɓar su, wanda ya haifar da musayar wuta.

A cewarsa, an kashe ’yan bindiga biyu, yayin da wasu kuma suka tsere  da yiwuwar harbin bindiga, inda suka bar alamar zubar jini a hanyoyin da suke bi.

Zhakom ya ƙara da cewa sojojin sun ƙwato makamai da alburusai a yayin samamen, waɗanda a halin yanzu suna hannunsu domin ci gaba da ɗaukar mataki yayin da sojojin ke bin sahun ’yan bindigar da suka tsere domin tunkarar su.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Bayan bayanan sirri kan shirin da ’yan bindiga suka yi na kai hari a ƙauyukan Nteng da ke Ƙaramar Hukumar Qua’an Pan ta Jihar Filato, sojojin 3 Division/Operation SAFE HAVEN sun yi wa maharan kwanton ɓauna, tare da tuntuɓar su yayin da suke tunkarar Unguwar Nteng.

“A yayin arangamar tare da musayar wuta a ranar Laraba, 16 ga Yuli, 2025, sojoji sun kashe ’yan bindiga biyu yayin da wasu kuma suka tsere da raunukan harbin bindiga kamar yadda aka gano tabon jini a hanyarsu ta tserewa daga yankin.”