✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da wasu kan zargin kashe matafiya bikin aure a Jos

An kashe mutum 13 daga cikin matafiyan, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da wasu da ake zargin ’yan daba ne suka…

Rundunar ’yan sandan Jihar Filato a ranar Alhamis ta gurfanar da wasu mutane 22 da ake zargi da kashe matafiya bikin aure a unguwar Mangun da ke Ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato.

An kashe mutum 13 daga cikin matafiyan, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da wasu da ake zargin ’yan daba ne suka kai lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa unguwar Qua da ke ƙaramar hukumar Qua’an Pan ta Jihar Filato.

Adadin waɗanda aka kashe mutum 32 da suka haɗa da maza da mata da ƙananan yara suna cikin wata mota ƙirar bas mai kujeru 18 daga unguwar Basawa da ke Ƙaramar hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna, domin halartar bikin aure a lokacin da suka haɗu da maharan.

Da yake gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban babbar kotun jihar, lauya mai shigar da ƙara, S.I. Ikutanwa, ya nemi izinin kotun domin waɗanda ake zargin su ɗaukaka ƙara kan tuhume-tuhume huɗu da ake yi musu.

Sai dai lauyan da ke kare waɗanda ake zargin Garba Pwol, ya ƙi amincewa da buƙatar ƙarar, inda ya ce biyu daga cikin mutum 22 ƙananan yara ne, wanda hakan ya sa tuhume-tuhumen ba su da tushe.

A cewar lauyan da ke kare waɗanda ake zargin ’yan shekaru 13 ne da kuma 17, kuma doka ba ta yarda a gabatar ƙananan yara a irin wannan shari’ar ba. Lauyan da ke kare waɗanda ake ƙara ya buƙaci kotun da ta ba shi lokaci domin shigar da ƙara.

Da yake mayar da martani ga lauyan waɗanda ake tuhuma, lauyan mai shigar da ƙara ya ce, tun da biyu daga cikin waɗanda ake zargin ’yan ƙasa da shekaru 18 ne a cire sunayensu, sannan a bar sauran mutum 20 da ake tuhuma su amsa tuhumar.

Da yake tsokaci kan sharia’ar ga ɓangarorin biyu da suka gabatar, alƙalin kotun, Mai shari’a Boniface Ngyon, ya ce zai fi kyau kada a shigar da ƙarar nasu ranar Alhamis, maimakon haka za a yi gyara a ranar Juma’a, ban da ƙananan yara.