Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan masu dawowa daga binne gawa a kauyen Rim na jihar Filato, inda suka datse wa daya daga cikin matasan da ke wurin hannu daya.
Bayanai sun nuna cewa mutanen na kan hanyarsu ce ta dawowa daga bikin binne wani mutum ne a kauyen Bachit da ke da makwabtaka da su inda suka yi arba da maharan wadanda suka tare su suka bude musu wuta, sannan suka datse wa daya daga cikin mutanen hannu daya.
- Rasha ta amince da gwamnatin Taliban a Afghanistan
- Ambaliya da iska sun rushe gidaje 171 a watanni biyu a Gombe – SEMA
Wani Hadimin Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, mai suna Timothy Dantong, wanda yake cikin mutanen da suke dawowa daga binnewar da shi ma ya tsallake rijiya da baya, ya tabbatar wa majiyarmu da kai harin a ranar Alhamis.
Ya ce daga bisani an turo wata tankar yaki da jami’an tsaro wadanda suka isa yankin suka ceto su.
Timothy ya ce, “Jiya na je jana’iza a kauyena na Bachit. A kan hanyarmu ta dawowa sai muka tarar an kai hari kauyen Rim, inda aka shawarce mu da mu dakata, saboda dole sai mun wuce ta nan kafin mu koma gida. Haka muka zauna sai da muka shafe awa biya muna zaman jira.
“Wasu daga cikinmu da suka gaza jira suka tafi, inda aka bude musu wuta sannan aka cire wa daya daga cikinsu hannunsa gaba daya.
“Mu ma dole sai daga baya aka turo mana tankar yaki ta zo ta ceto mu daga zaman jiran tsammani, amma da tuni lamarin ya ritsa da ni. Ban son me wadannan maharan suke so daga gare mu ba, sun matsa wa mutanenmu,” in ji Timothy.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, Alabo Alfred bai dauki kiran da aka mas aba don jin ta bakin rundunar kan harin, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.