Wasu da ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa ne, sun kai hari ƙauyen Kwalajiya da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutum 15.
Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Talata, lokacin da mutum ke sallar Azahar.
- NAJERIYA A YAU: Ɓoyayyun Ƙalubalen Da Sabuwar Haɗakar ADC Za Ta Iya Fuskanta
- An sa zare tsakanin ‘yan Kannywood da Alhikima
Rahotanni daga mazauna yankin sun ce harin ramuwar gayya ne bayan da al’ummar ƙauyen suka daƙile wani hari da aka kai musu kwanakin baya, inda suka kashe ’yan ta’addan Lakurawa uku ciki har da wani jagoransu.
A wannan sabon harin, ’yan bindigar sun dawo da yawa inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi.
“Muna cikin Masallaci muna sallah suka shigo suka fara harbinmu,” in ji wani mazaunin ƙauyen.
“Sun kashe mazajenmu, sun kuma ƙone kayayyakin abinci da shaguna da gidaje.”
’Yan bindigar sun kuma ƙone gonaki da na’urorin sadarwar ƙauyen, sun lalata turakun layin sadarwa, wanda hakan ya sa ba a iya kiran waya waya ko hanyoyin sadarwa.
Yawancin mazauna ƙauyen sun tsere zuwa garuruwan Gidan Madi da Sakkwato domin neman ɗauki.
“Ina zama yanzu da ’yan uwana a cikin gari,” in ji wata mata.
“Muna roƙon gwamnati ta kawo mana jami’an tsaro, ta kuma dawo mana da layin sadarwa domin mu riƙa bayar da rahoton ayyukan ’yan bindigar.”
Wasu mazauna yankin na zargin cewa harin yana da nasaba da yadda ƙauyen ke bijirewa yawaitar tasirin ƙungiyar.
Wani jagoran al’umma ya taɓa gargaɗin mutane da kada su yadda ’ya’yansu mata su auri ’yan ƙungiyar, wanda hakan ya fusata su.
Wani jami’in Ƙaramar Hukumar ya tabbatar da mutuwar mutum 15 tare da raunata wasu bakwai.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar dai ta ce suna nan suna bincike, amma tuni aka tura jami’an tsaro zuwa yankin domin daƙile karin hari.
Ba wannan ne karon farko da ƙungiyar Lakurawa ke kai hari a yankin ba.
A makon da ya gabata, sun kashe mutum takwas a Sabiyo, kuma sun kai hari ƙauyen Baiji.
Haka kuma sun dasa bam a wani waje da ya kashe aƙalla mutum bakwai a garin Gwabro.
“Wannan ’yan ta’adda suna aiki ba tare da ƙaƙƙautawa ba,” in ji Ghazali Rakah, hadimin Shugaban Ƙaramar Hukumar.
“Sun kusan shiga Sanyinna amma suka janye bayan ganin zuwan sojoji.”
Ƙwarrarren masani kan sha’anin tsaro, Squadron Leader Aminu Bala Sakkwato (mai ritaya), ya buƙaci Gwamnatin Sakkwato da ta horar da matasa domin su taimaka wajen kare ƙauyuka da ke da hatsarin fuskantar hare-haren ’yan ta’adda.
“Rundunar tsaro ta ƙasa na da tarin aiki. Muna buƙatar matasa da aka horas, tare da haɗin gwiwar sojoji domin daƙile barazanar,” in ji shi.
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ce tana aiki kafaɗa da kafaɗa da rundunar soji da ’yan sanda domin inganta tsaro a yankin Tangaza da kewaye.