Uwargidan shugaban ƙasa, Remi Tinubu ta bayar da gudummawar Naira biliyan ɗaya ga waɗanda harin ya rutsa da su a wasu yankunan Jihar Filato.
Uwargidan shugaban ƙasar wacce ta bayyana bayar da tallafin a yayin ziyarar jaje da ta kai jihar a ranar Alhamis, ta ce kuɗaɗen da ta bayar ba na gwamnati ba ne, kuɗin ta ne da ta tara don taimakawa wasu.
- Buhari ba ya cikin mawuyacin hali — Bashir Ahmad
- ’Yan Majalisar Wakilai bakwai na Akwa Ibom sun koma APC
“A yau na zo da gudunmawar Naira biliyan 1 don shirin sabuwar Najeriya (Renewed Hope Initiative), ba ni da maƙudan kuɗaɗe, amma abin da nake da shi shi ne in taimaki rayuwar wasu, ba wai in zuba kuɗi a kwandon ajiya ba.
“Idan da na ajiye kuɗi don amfanin kaina, hakan zai taimaka ne kawai don biyan buƙata ta kawai, amma burina shi ne in yi amfani da kadarar da nake da su wajen kyautatawa ƙasar nan, don ci gaban ƙasar nan, ba wai in ɓarnatar da su ba.
“Don Allah ku fahimci cewa kuɗin da nake da shi na wannan shiri ba na gwamnati ba ne, kuɗi ne na kaina da na tara don in taimaka wa wasu, yayin da nake ci gaba da tafiye-tafiye na ga tasirin ayyukanmu, ina roƙon ku da ku yi addu’a domin mu kawo canji mai ɗorewa.
“Na yi ta addu’a musamman ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a wasu wurare ma, na yi ta addu’a cewa damina ta ciyar da ƙasa da abinci kada ta lalata amfanin gonar, Ubangiji ya ji addu’armu, kuma za mu ziyarci wasu wuraren da ake buƙatar tallafi kamar Binuwai da Neja.