✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsare mutum 20 da ake zargi da kisan ’yan ɗaurin aure a Filato

Kotun ta aike su gidan yari zuwa lokacin da za ta sake zama.

Wata Kotu a Jos, Babban Birnin Jihar Filato, ta tura mutum 20 da ake zargi da kisan ’yan ɗaurin aure a Jihar Filato zuwa gidan yari.

Ana zarginsu da kashe wasu ’yan ɗaurin aure a ƙauyen Mangun da ke Ƙaramar Hukumar Mangu a jihar.

Mutanen da aka kashe suna cikin wata motar haya da ta taso daga Basawa a Karamar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna.

Baƙin suna kan hanyarsu ta zuwa ƙauyen Kwa a Ƙaramar Hukumar Qua’an Pan da ke Jihar Filato domin halartar ɗaurin aure.

Wasu ɓata-gari ne suka kai musu hari.

Ɓata-garin sun kashe mutum 13, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Mata, maza da yara na cikin motar wadda ke ɗauke da fasinjoji 32.

A ranar Alhamis, ‘yan sanda suka gurfanar da mutum 22 a kotu bisa zargin kashe baƙin.

Amma kotu ba ta bayyana matsayinta ba saboda lauyan da ke kare waɗanda ake zargin, Garba Pwul, ya ce akwai yara ƙanana guda biyu a cikinsu ɗaya yana da shekaru 13, ɗaya kuma shekaru 17 kuma bai kamata a gurfanar da su ba.

Alƙalin kotun ya amince da hakan kuma ya umarci ’yan sanda su cire su daga cikin jerin waɗanda aka gurfanar.

An sake gurfanar da mutum 20

A ranar Juma’a, ’yan sanda suka sake gurfanar da sauran mutum 20.

Ana tuhumar su da laifuka guda hudu: haɗa kai wajen aikata laifi, jikkata mutane, kisa, da ƙone gawarwakin mutum 13 a ranar 20 ga watan Yuni, 2025.

’Yan sanda sun ce waɗanda ake zargin sun yi amfani da makamai masu hatsari kamar bindiga, adda, takobi da man fetur.

Dukkanin mutum 20 da ake tuhuma sun ce ba su da laifi.

Bayan sun bayyana matsayinsu, lauyan ’yan sanda ya roƙi kotu da ta tura su gidan yari tare da ɗage shari’ar zuwa wani lokaci.

Lauyan da ke kare su ya nemi a ba da belinsu, amma lauyan gwamnati ya ce bai da isasshen lokaci don ya amsa wannan buƙata bisa doka.

Alkalin kotun, Mai shari’a Boniface Ngyong, ya ce ba za a saurari buƙatar belin a yanzu ba, saboda ƙorafin da lauyan gwamnati ya gabatar.

Ya ɗage shari’ar zuwa ranar 13 ga watan Agusta, 2025, sannan ya umarci a ci gaba da tsare su a gidan yari na Jos.