✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu ƙwacen waya sun kashe ma’aikaciyar ofishin jakadancin Ghana a Abuja

Masu kwacen da aka fi san da ’yan ‘One Chance’, sun kashe Freda Arnong, wata ma’aikaciya a ofishin jakadancin kasar Ghana da ke babban birnin…

Masu kwacen da aka fi san da ’yan ‘One Chance’, sun kashe Freda Arnong, wata ma’aikaciya a ofishin jakadancin kasar Ghana da ke babban birnin tarayya Abuja.

Bayanai sun nuna matar, wacce daga bisani ta mutu a asibitin kasa da ke Abuja, ta hau motar da ake zargin ta masu kwacen ce a bisa rashin sani.

Wata majiya daga jami’an tsaro ta shaida wa wakilinmu cewa Freda ta hau motar ta tasi ne daga marabar otal din Transcorp a makon da ya gabata.

Majiyar ta ce a lokacin da matar ta shiga, akwai wasu mutum hudu da har yanzu ba a kai ga tantance su ba.

Majiyar ta ce daga nan ne sai direban motar ya canza hanya ya bi titin zuwa Lugbe-filin jirgin sama, inda suka kashe ta, kafin daga bisani su jefar da gawarta yayin da motar ke ci gaba da tafiya.

Daga nan ne aka dauke ta aka garzaya da ita asibitin, inda daga bisani ta rasu a ranar Talata.

Ita ma wata majiya daga asibitin da ta ce ba ta da hurumin yin magana da ’yan jarida ta tabbatar da mutuwar matar.

“Ta mutu wajen misalin karfe 1:52 na ranar Talata, kuma yanzu haka gawarta tana dakin adana gawarwaki na asibitin domin yin binciken musabbabin mutuwar tata,” in ji majiyar.

Sai dai da wakilinmu ya tuntubi Kakakin rundunar ’yan sanda ta yankin Abuja, SP Adeh Josephine, amma ba ta amsa kira ko sakon kar-ta-kwanan da ya tura mata ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.