✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Ya’yana na da ’yancin mallakar filaye a Abuja – Wike

ministan Babban Birninn Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya musanta labarin cewa ya yanka wa ’ya’yansa manyan filaye a Abuja, inda ya ce in ma haka…

Ministan Babban Birninn Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya musanta labarin cewa ya yanka wa ’ya’yansa manyan filaye a Abuja, inda ya ce in ma haka ne suna da hakki a matsayinsu na ’yan Najeriya.

Ana dai zargin Wike da ba biyu daga cikin ’ya’yansa fili mai fadin murabba’in hekta 2,082, dayan kuma mai fadin hekta 1,740, wanda aka kiyasta darajarsu ta haura Naira tiriliyan tara.

Da yake zantawa da ’yan jarida a Abuja ranar Alhamis, Wike ya karyata labarin na cewa ya ba ’ya’yan nasa filayen a unguwannin Maitama da Asokoro.

To sai dai duk da haka, ya kare batun, inda ya ce a matsayin su na ’yan Najeriya, su ma sun cancanci su mallaki filayen matukar dai an bi ka’ida.

“Alal misali, amma ba wai na amsa haka ba ne, a ce ’ya’yana sun nemi filayen, shin ba su cancanta a ba su ba ne? ko su ’yan Ghana ne? ko kuwa a’a, kawai saboda ni ina minista shi ke nan ba su cancanta ba?,” in ji Wike.

Ministan ya zargi wasu mutane da ya ce ba su da suna daga jihar Adamawa da kitsa zancen domin kawai su bata masa suna.

“Da farko ma ka fara lissafa hekta 2,000 na fili sai ka fada min a ina za ka sami hakan a Asokoro da Maitama. Na san daga jihar Adamawa aka shirya wannan kitimurmurar,” in ji shi.