✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ribas: Duk wani rikici tsakanina da Fubara ya ƙare – Wike

Yanzu ɓangarorin biyun sun amince su yi aiki tare domin ci gaban Jihar Ribas.

Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya tabbatar da cewa tattaunawar da suka yi da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta kawo ƙarshen duk wata rigima da ke tsakaninsa da Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara.

A daren ranar Alhamis ne Shugaba Tinubu, ya jagoranci wani zaman sulhu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, tsakanin Wike da Gwamna Fubara da kuma wasu daga cikin ’yan majalisar Ribas da aka dakatar.

Bayan ganawar, Wike ya yi magana da manema labarai, inda ya tabbatar da kawo ƙarshen rikicinsa da Fubara.

“Dukkaninmu mun amince mu yi aiki tare da Gwamna, kuma shi ma ya amince zai yi aiki da mu. Dukkanninmu ’yan gida ɗaya ne.

“Rigimarmu ta daɗe, amma zamanmu na ranar Alhamis ya kawo ƙarshenta. Dama ɗan Adam yana iya samun saɓani, amma daga baya a sasanta.”

Ya ƙara da cewa: “Kuma yau ne muka kammala komai, mun zo mun shaida wa Shugaban Ƙasa cewa mun daidaita. Don haka a gare ni, komai ya wuce.”

Wike, ya kuma yi kira ga mabiyansa da su kwantar da hankali tare da haɗa kai don ciyar da Ribas gaba.

“Ina kira ga kowa da kowa da mu haɗa kai da sauran jama’a. Babu sauran rigima, babu wani abu da za a sake yin faɗa a kai.”

Abin da rikicin ya haifar

A baya dai rikicin siyasa a Jihar Ribas, ya haifar da barazanar tsige Gwamna Fubara a watan Oktoban 2024, yayin daga bisani Shugaba Tinubu ya ayyana  dokar ta-ɓaci a watan Maris a jihar

Sai dai yanzu ɓangarorin sun ce komai ya wuce, kuma za su ci gaba da aiki tare domin ci gaban jihar.