Shugaban Ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa ƙasarsa za ta ci gaba da mayar da martani kan hare-haren da Isra’ila ke kai mata.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake magana da shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ta wayar tarho.
- Uba Sani ya yi jajen ’yan ɗaurin aure 12 da aka kashe a Filato
- Ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe mutum 10 da bam a Borno
Shugaba Pezeshkian ya ce Iran tana da niyyar yin haɗin gwiwa da sauran ƙasashe don amfani da makamashin nukiliya ta hanyar da ba ta da alaƙa da yaƙi, amma hakan ba yana nufin za su dakatar da inganta shirye-shiryensu na nukiliya gaba ɗaya ba.
Ya ƙara da cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa ƙasarsa ba za su wuce haka nan ba, domin kuwa Iran za ta riƙa mayar da martani mai zafi.
A ranar Asabar, rundunar sojin Iran ta yi gargaɗi cewa za ta kai wa Isra’ila ta hark ta jiragen ruwa.
A cewar wani kakakin rundunar sojin Iran da ya bayyana a wani bidiyo, duk ƙasar da ta tura makamai zuwa Isra’ila, kamar ta shiga yaƙi da Iran ce kai-tsaye, kuma Iran ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kare kanta ba.
A ranar Juma’ar da ta gabata, Iran ta harba makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa zuwa Isra’ila, lamarin da ya jikkata mutane aƙalla 19 a birnin Haifa da ke Arewacin Isra’ila, kamar yadda wani asibiti a yankin ya tabbatar.