✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ministan Harkokin Wajen Iran ya isa taron Kungiyar OIC a Turkiyya

Ministan Harkokin Wajen ƙasar Iran ya isa ƙasar Turkiyya domin halartar taron Ƙungiyar Haɗin kan Kasashen Musulmi (OIC) a ranar Asabar.

Wakilin ƙasar Iran ya isa birnin Santanbul na ƙasar Turkiyya domin halartar taron Ƙungiyar Haɗin kan Kasashen Musulmi (OIC) a ranar Asabar.

Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito cewa, a yayin taron Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, zai gana da jami’an diflomasiyya na ƙasashen Larabawa don tattauna batun rikicin da ke ƙara ƙamari tsakanin ƙasarsa da Isra’ila.

Kimanin jami’an diflomasiyya 40 ne ake sa ran za su halarci taron a daidai lokacin da Isra’ila da Iran ke ci gaba da musayar hare-haren makamai masu linzami.

“Ministan harkokin wajen ya isa Istanbul a safiyar yau domin halartar taron ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan Musulunci,” in ji Tasnim.

Wannan ziyarar ta zo ne bayan da Ministan ya gana da takwarorinsa daga Biritaniya, Faransa, da Jamus a Geneva a ranar Juma’a.

A cewar kamfanin dillancin labaran, “A wannan taron, bisa shawarar Iran, za a tattauna batun harin da gwamnatin Isra’ila ta kai wa kasarmu musamman,” in ji Araghchi.

Isra’ila ta fara farmakinta ne a safiyar 13 ga watan Yuni, tana mai cewa Iran tana dab da ƙera makaman nukiliya.

Wannan ya haifar da martani nan take daga Tehran, a rikici mafi mubi da aka taɓa fuskanta tsakanin kasashen biyu masu zaman doya da manja.

Tun da farko a ranar Juma’a, Araghchi ya bayyana cewa Iran a shirye take ta “sake duba harkokin diflomasiyya” idan har “aka dakatar da hare-haren Isra’ila.”

Ana sa ran ministocin ƙasashen Larabawa za su fitar da sanarwa bayan ganawarsu, in ji kamfanin dillancin labarai na ƙasar Turkiyya Anadolu.