✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nan da mako biyu za mu yanke shawara kan shigar wa Isra’ila yaƙi — Trump

Trump ya kuma ce akwai yiwuwar a zauna a teburin sulhu.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce sai nan da mako biyu zai yanke shawara kan ko zai shigar wa Isra’ila yaƙin da take yi da Iran ko kuma akasin haka.

A wata sanarwa da sakatariyar yaɗa labaran fadar gwamnatin Amurka, Karoline Leavitt ta karanto, Trump ya ce akwai yiwuwar a zauna a teburin sulhu.

Waadin yanke shawarar da Trump ya bayar na zuwa ne bayan kwanaki ana rade-radin cewa Amurka za ta shigar wa Isra’ila yaƙin da ta ƙaddamar don ganin ta hana Iran mallakar makaman nukiliya.

Trump dai ya shafe makonni yana bibiyar hanyar diflomasiyya don cimma yarjejeniyar nukiliya da Iran wadda ya soma tattaunawa da ita tun a wa’adinsa na farko a shekarar 2018.

Sai dai duk da haka, Trump ya yi maraba da hare-haren da Isra’ila ta kaddamar musamman kan cibiyoyin nukiliyar Iran da manyan sojojinta.

A jiya Laraba ce Trump ya bayyana cewa ya san inda jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei yake “boye”, kuma ya yi gargadi cewa Washington na iya halaka shi, amma za su dakata a halin yanzu.

Trump din ya kuma shaida wa Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu cewa kashe Khamenie “ba shawara ce mai kyau ba.”

Tun tsawon kwanaki bakwai, Isra’ila ke kai hare-hare a cikin Iran, da suka shafi wuraren nukiliya da manyan kwamandojin soji da masana kimiyya da cibiyoyin tsaro da birane da ma cibiyoyin mai da iskar gas.

Iran dai ta mayar da martani da makamai masu linzami gami da jirage masu sarrafa kansu a kan Isra’ila, lamarin da ke kara fargabar cewa Amurka za ta iya shiga cikin rikicin kai tsaye, wanda kuma zai iya haifar da sabon babi mai hadari a rikicin.

Birtaniya ta gargadi Trump kan shigar wa Isra’ila

Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya buƙaci Donald Trump kada ya ɗauki matakin soji kan Iran, yana mai kiran da a biyo wa lamarin ta hanyar lalama.

Mista Starmer ya ce akwai “mummunan hatsarin bazuwar” yaƙin, inda ya yi kira ga duka ɓangarorin sun rungumi sulhu.

Ya ƙara da cewa a baya an samu “jerin tattauna masu yawa da Amurka, kuma ina ganin wannan ita ce hanyar warware matsalar.”

Kalaman nasa na zuwa ne yayin da sakataren harkokin wajensa, David Lammy ke shirin ganawa da takwaransa na Amurka, Marco Rubio kan yadda za a taƙaita bazuwar yaƙin.