Iran ta lalata cibiyar binciken kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila, wato cibiyar kimiyya ta Weizmann Institute of Science da ke birnin Tel Aviv.
Cibiyar, wadda ke da alaƙa da binciken harkokin sojin Isra’ila, ta sanar da cewa harin da Iran ta kawo ɗin ya yi sanadiyar ɓarnar da ta kai kimanin Dala miliyan 500.
Makaman Iran sun lalata gine-gine da dama a cibiyar, lamarin da ya sanya masu bincike faɗi-tashi don ceto samfurin bincike a cikin ɓaraguzan gini, a yayin da gobarar ke ci.
Wani makami mai linzami ya tarwatsa wani gini mai ɗauke da ɗakunan gwaje-gwaje na zamani da dama, a yayin harin na ramuwar gayya, bayan da Isra’ila ta kashe masana kimiyyar nukiliya na Iran.
- 2027: Manyan ’Yan adawa na neman rajistar sabuwar jam’iyya
- Wani ya kashe mahaifiyarsa mai shekara 71 a Akwa Ibom
Makamin ya faɗo kan cibiyar ne kafin wayewar garin ranar Lahadi, amma babu wanda ya ji rauni domin cibiyar ba kowa a cikinta a lokacin.
Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya ziyarci wurin, inda ya ce, “wannan harin ne dalilin da ya sa Isra’ila ba za a taɓa barin Iran ta mallaki makaman nukiliya ba.”
Idan ba a manta ba, Isra’ila ce ta fara kai hari kan Iran a ranar 13 ga Yuni, bisa hujjar cewa abokiyar gabar tata tana dab da ƙera makaman nukiliya.
Iran, wadda ta dage cewa shirin nukiliyarta don dalilai na zaman lafiya ne kawai, ta mayar da martani da hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa a kan Isra’ila.
Hare-haren Isra’ila sun yi sanadiyar mutuwar wasu manyan masana kimiyyar nukiliya na Iran, da manyan shugabannin sojojin Iran, da fararen hula tare da lalata gidaje da tashoshin nukiliya da ababen more rayuwa.
Duk da cewa yawancin binciken cibiyar Weizmann sun danganci fannin gas magunguna da ilimin kimiyya ne, amma tana kuma da alaka da tsaro.
A watan Oktoba na 2024, ta sanar da haɗin gwiwa da babban kamfanin tsaro na Isra’ila, Elbit, kan “kayayyakin da aka samo daga halittu don aikace-aikacen tsaro.”
Cibiyar binciken kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila, tana da ƙungiyoyin bincike 286, masana kimiyya ma’aikata 191, da daruruwan dalibai.
Iran ta sanar a ranar Juma’a cewa ba za ta tattauna makomar shirin nukiliyarta ba yayin da take fama da hare-hare daga Isra’ila.
Duk ƙoƙarin ƙasashen Turai na jan hankalin Tehran zuwa tattaunawa bai nuna alamun nasara ba.