✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu iya galaba kan Iran ko babu Amurka — Isra’ila

Babbar nasarar da za mu samu ita ce kawo ƙarshen barazanar nukiliyar Iran.

Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, ya bayyana cewa ƙasarsa za ta iya samun nasara a yaƙin da take yi da Iran ko da kuwa Amurka ba ta shigar mata ba.

Sai dai Herzog ya shaida wa ABC News cewa kawar da barazanar nukiliyar Iran yana da muhimmanci ga “duniya mai ’yanci”, ciki har da Amurka.

Da yake amsa tambayar ko me zai ce dangane da yiwuwar shigar wa ƙasarsa yaƙin da take yi da Iran da Shugaba Donald Trump ya yi iƙirari, Herzog ya ce “ina da cikakkiyar yarda a kan duk wani hukunci da zai yanke kuma ina da tabbacin duk abin da ya yanke shi ne daidai.

Herzog ya ce mako guda ke nan da fara yaƙin amma ya tabbatar da cewa barazanar Iran ba za ta kau ba nan take.

“Babbar nasarar da za mu samu ita ce kawo ƙarshen barazanar nukiliyar Iran,” a cewar Herzog.

“[Jagoran addini na Iran, Ayotallah Ali Khamenei] shi ne kan macijin da ke jagorantar duk wata barazana da Iran take yi da muke buƙatar mu sare.

“Tun ba yanzu ba yake babatun ganin bayan ƙasarmu da al’ummarta. Saboda haka ba mu da wata manufa a yanzu face mun yi maganinsa,” kamar yadda Herzog ya shaida wa gidan talabijin na ABC.