Wata kotu a kasar Amurka ta yanke wa wasu ’yan Najeriya su biyar hukuncin daurin shekaru 159 bisa samun su da da laifin damfarar Amurkawa sama da 100.
Kotun dai ta sami mutanen ne da laifin damfarar kamfanoni da hukumomin gwamnatin kasar kudin da yawansu ya kai Dala miliyan 17, kwatwankwacin Naira biliyan 27 da miliyan 200.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sashen shari’a na kasar ya wallafa a shafinsa na intanet ranar Laraba, mai dauke da sa hannun mai rikon mukamin Babban Lauyan gwamnati na gundumar gabashin Texas, Ray Combs.
Sanarwar ta ce mutanen da aka yanke wa hukuncin sun hada da Damilola Kumapayi, Sandra Iribhogbe, Edgal Iribhogbe, Chidindu Okeke and Chiagoziem Okeke, kuma mambobi ne a wani gungun ’yan damfara na kasa da kasa.
Lauyan ya ce ’yan damfarar sun fara harkallar ne tun a shekara ta 2017, inda suke hakon tsofaffi da kuma masu rangwamen gata ta hanyar kirkiro dabaru daban-daban na karbar kudi daga wajensu, wasu lokutan ma ilahirin abin da suka tara a rayuwarsu.
“Da zarar sun karbi kudade daga mutane ta hanyar damfarar, sai su tuttura su ta hanyar asusun ajiya a bankuna da dama da kuma abokan harkallarsu da ’yan kasuwa da ke kasashe a nahiyoyin Afirka da Asiya,” in ji lauyan na gwamnatin Amurka.
Sanarwar ta ce bayan kama su, an gurfaran da su a gaban kotu kan laifukan da suka hada da hadin baki, zambar kudade da kuma damfara, wadanda dukkansu suka amsa aikatawa.
A cewar sanarwar, hakan ce ta sa alkalin kotun, Mai Shari’a Amos Mazzant, ya yanke musu hukuncin daurin shekaru daban-daban a kurkuku.