Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ya san inda jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei yake “boye”, kuma ya yi gargadi cewa Washington na iya halaka shi, amma za su dakata a halin yanzu.
Wannan na zuwa ne yayin da Trump din ya gargadi Iran kan da kada ta kai harin makamai masu linzami kan fararen hula ko kuma sojojin Amurka, yana mai cewa hakurinsu na karewa.
- Iran ta kai hari hedikwatar hukumar leƙen asirin Isra’ila
- Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mutum 20 a Chadi
A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Truth mintuna kadan bayan wannan sako, Trump ya rubuta cewar Iran din ta mika wuya ba tare da wani sharadi ba kawai.
Rahotanni a bayan nan sun ce Trump ya ƙi amincewa da shirin Isra’ila na kashe jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, kamar yadda majiyoyi uku suka shaida wa kafar yaɗa labarai ta CBS News.
Bayanan sun ce Shugaba Trump ya shaida wa Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu cewa kashe Khamenie “ba shawara ce mai kyau ba.”
Tattaunawar ta faru ne bayan harin da Isra’ila ta ƙaddamar kan Iran a ranar Juma’a.
A lokacin wata tattaunawa da kafar yaɗa labarai ta Fox News, Netanyahu bai fayyace kai-tsaye ko Trump ya ƙi amincewa da shawarar kashe Ayatollah ba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
“Akwai rahotannin da dama kan tattaunawar da ake cewa an yi amma kuma ba gaskiya ba ne, ba zan shiga cikin irin wannan maganar ba,” in ji Firaiminstan Isra’ila.
Tun tsawon kwanaki biyar, Isra’ila ke kai hare-hare a cikin Iran, da suka shafi wuraren nukiliya da manyan kwamandojin soji da masana kimiyya da cibiyoyin tsaro da birane da ma cibiyoyin mai da iskar gas.
Iran dai ta mayar da martani da makamai masu linzami gami da jirage masu sarrafa kansu a kan Isra’ila, lamarin da ke kara fargabar cewa Amurka za ta iya shiga cikin rikicin kai tsaye, wanda kuma zai iya haifar da sabon babi mai hadari a rikicin.
A gefe guda kuma, babban hafsan tsaron Iran ya yi gargadi ga mazauna Isra’ila “musamman ma na biranen Tel Aviv da Haifa da su gaggauta barin wurarensu don tsira da rayukansu.
Janar Abdolrahim Mousavi, ya ce ayyukan da aka gudanar zuwa yanzu sun kasance gargadi ne kan abin da ke tafe, kuma za a gudanar da wani aiki na ladabtarwa nan ba da jimawa ba daga Iran.
Koda yake hare-haren Iran sun kashe akalla Isra’ilawa 24 tun a ranar Juma’a, galibin makaman Iran din dai Isra’ila ta dakatar da su ta hanyar tsarin kariyarta ta sama.