Iran ta kai hari a kan hedikwatar hukumar leƙen asiri ta ƙasar Isra’ila (Mossad) kamar yadda kafofin yaɗa labarai na cikin gida a Iran suka ruwaito a ranar Talata.
Kamfanin dillancin labaran Iran (TASNIM) ya ba da rahoton cewa rundumar juyin juya hali na Iran (IRGC) ce ta kai harin a hedikwatar Mossad da ke Herzliya.
Tasnim ya wallafa wasu jerin hotuna da ya ce suna nuna yadda hedikwatar ta Mossad ke ci da wutan ne bayan harin makamai masu linzami ne da Iran ta kai mata.
Kafar yaɗa labarai ta Tehran Times ta ruwaito cewa hare-haren na IRGC sun ƙona wani ɓangare na cibiyar Aman, wanda wani ɓangare ne na ginin hukumar leƙen asirin asirin sojin Isra’ila ta Aman, da ke Glilot.
- An garzaya da ’yan Isra’ila 154 asibiti bayan harin Iran
- Matatar man Isra’ila ta daina aiki bayan sabon harin Iran
- Sarki ya yi barazanar hana yin Musulunci a garinsa bayan dodanni sun kai wa Musulmi hari
Kawo yanzu dai ba a iya tantance sahihancin wannan iƙirarin na Iran ba daga kafofin yaɗa labarai da ke aiki a yankin; kuma hukumomin Isra’ila ba su ce uffan a kai ba.
A cewar hukumar kare haƙƙin ɗan’Adam a Iran (HRANA), fararen hula 224 ne suka mutu, yayin da 188 suka jikkata a hare-haren Isra’ila a ƙasar.
HRANA ta kuma bayyana cewa sojoji 109 ne suka mutu inda kuma 123 suka jikkata.