✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tankokin Isra’ila sun kashe mutum 51 a wurin karbar abinci a Gaza

Jami’ain lafiya sun sun ce mutum 51 sun mutu, wasu 200 sun samu raunuka — 20 daga cikinsu suna cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai — bayan harin.

Tankokin yaƙin Isra’ila sun i kashe kimanin mutun 51 a yankin Khan Younis da ke Zirin Gaza, a yayin da mutanen suke tsaka da karbar abincin tallafi.

Jami’ain lafiya sun sun ce mutum 51 sun mutu, wasu 200 sun samu raunuka — 20 daga cikinsu suna cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai — bayan harin.

Sun bayyana harin a matsayin daya daga cikin mafiya muni da sojojin Isra’ila suka kai a baya-bayan nan a yayain da Falasdinawa ke kokarin samun abinci domin su rayu.

Bidiyon lamarin da suka karade kafofin sada zumunta sun nuna wasu gomman gawarwaki da ake zargin tankokin yakin Isra’ila sun mutsuttsuke a kan titi a Khan Younis.

Shaidu sun bayyana cewa sai da sojojin Isra’ilan suka sa mutanen suka taro a wuri guda sa’annan tankokin suka bude musu wuta.

Tankokin sun bude wuta ne a daidai lokacin da suke kokarin karbar tallafin abinci daga wata babbar motar kungiyar agaji.

Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da aukuwar harin na ranar Litinin, wanda ta ce tana gudanar da bincike a kai.