✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaƙin Iran da Isra’ila: Amurka za ta tura jami’anta don tattaunawa da Tehran

Trump ya ce yana neman ganin an kawo karshen rikicin nukiliyar ƙasar Iran gaba ɗaya, a yayin da aka shiga kwana na biyar a yaƙin…

Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump ya ce yana neman ganin an kawo karshen rikicin nukiliyar ƙasar Iran gaba ɗaya, a yayin da aka shiga kwana na biyar a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra’ila. 

Trump ya bayyana shirinsa na tura manyan jami’an ƙasarsa zuwa birnin Tehran domin tattaunawa da hukumomin Iran a game da lamarin.

Ya bayyana haka ne a yayin da yake hawa jirgi domin barin ƙasar Kanada, inda ya halarci taron ƙasashen G7.

A yayin taron, shugabannin ƙasahen sun bayyana Iran a matsayin barazana, da bai kamata a bari ta mallaki makaman nukiliya ba. A ɗaya bangaren kuma sun bayyana ’yancin Isra’ila na kare kanta.

Trump wanda ya bar taron tun kafin a kammala ya bayyana cewa abin da ke gabansa na wuce batun tsagaita wuta da Amurka ke nema  tsakanin Iran da Isra’ila.

Ya bayyana cewa ƙasashen biyu da a halin yanzu suke ci gaba da yi wa juna luguden bama-bamai ba su sassauta ba, amma ya sha nanata cewa akwai yiwuwar kawo ƙarshen rikicin da wuri, idan Iran ta amince da tayin da Amurka ta yi mata.

Makon jiya ne jiragen Isra’ila suka ƙaddamar da hare-haren ba-zata a Iran inda suka kashe wasu manyan kwamandoji da masana kimiyyar nukiliya.

Isra’ila ta yi iƙirarin karɓe ikon sararin samaniyar Iran, kuma za ta tsananta kai hare-hare a nan gaba.

Hare-haren sun halaka mutane da dama a sassan kasashen biyu.

Rahotanni a cikin dare sun nuna yadda na’urorin tsaron sararin samaniyar Iran ke kakkaɓo makamai a sassan ƙasar.

Rundunar juyin juya halin Musulunci na Iran ta bayyana cewa za ta sake harba tarin rokoki zuwa Isra’ila.