Iran ta kai sabbin hare-hare kan manyan biranen Isra’ila da suka haɗa da Tel Aviv da Haifa, inda ta yi amfani da makaman linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa.
A cewar gidan talabijin na Iran, gomman makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa ne suka tashi zuwa Isra’ila, kuma wasu daga cikinsu sun ƙetare garkuwar kariyar iska ta Isra’ila.
- An tallafa wa mata 250 da abinci da kayan sana’a a Kaduna
- Yadda wani ɗan sanda ya rasu a hanyar zuwa ɗaurin aurensa
Sai dai har yanzu ba a ji wani bayani daga sojojin Isra’ila ba.
Faɗan Iran da Isra’ila ya fara ne bayan Isra’ila ta kai hari kan wani sashen ofishin jakadancin Iran da ke birnin Damascus na Siriya, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu manyan jami’an Iran.
Wannan mataki ya tayar da hankalin Iran, inda ta sha alwashin ramawa kuma wannan hari da ta kai yanzu na daga cikin mayar da martani kan harin Isra’ila.