An shiga zaman ɗari-ɗari a garin Makurdi na Jihar Benuwe, bayan ’yan sanda sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa wasu masu zanga-zanga a shataletalen Wurukum.
Masu zanga-zangar sun fara taruwa da misalin ƙarfe 9:30 na safe domin nuna fushinsu kan kisan mutane sama da 100 a garin Yelewata da ke Ƙaramar Hukumar Guma, a ranar Asabar.
- Takarar Tinubu: Rikici ya ɓarke a APC bayan Ganduje ya ƙi goyon bayan Shettima
- HOTUNA: Yadda aka yi sulhu da ƙasurgumin ɗan fashin daji Ado Aliero a Katsina
Tun kafin fara zanga-zangar, jami’an tsaro daga hukumomi daban-daban sun mamaye manyan hanyoyi a birnin Makurdi.
Da safiyar ranar Lahadi da misalin ƙarfe 7 na safe jami’an tsaro, ciki har da motar yaƙi ta ‘yan sanda sun yi wa wajen tsinke.
An kuma hango sojoji a gadar kusa da wajen, yayin da jami’an NDLEA, NSCDC da sauran hukumomi suka kasance ɗauke da manyan makamai.
Rahotanni sun nuna cewa wannan matakin tsaro an ɗauke shi ne don hana zanga-zangar, amma da mutane suka fara taruwa, ‘yan sanda sun harba barkonon tsohuwa da misalin ƙarfe 11 na safe domin tarwatsa su.
Duk da haka, masu zanga-zangar ba su karaya ba, yayin da wani shahararren mai fafutuka a kafafen sada zumunta, VeryDarkMan, ya jagoranci zanga-zangar.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Ifeanyi Enemari, ya isa wajen zanga-zangar sannan ya roƙi matasan da ke zanga-zangar da su zauna lafiya.
Ya ce jami’an tsaro na bakin ƙoƙarinsu don kawo ƙarshen kashe-kashen da ke faruwa a jihar.
Ya bayyana cewa Sufeto Janar na ’Yan Sanda ya tura rundunoni na musamman zuwa jihar domin taimakawa wajen tsaro, kuma wasu daga cikinsu sun isa jihar, sauran kuma na hanya.
Kwamishinan ya ce gwamnati ta bai wa jami’an tsaro goyon baya sosai kuma an riga an kama wasu.