✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wutar lantarki ta kashe mutum 5, ta jikkata 13 a Gombe

Wutar ta tashi ne sakamakon matsala da aka samu yayin kawo wutar lantarki.

Rundunar ’Yan Sandan jihar Gombe, ta tabbatar da mutuwar mutum biyar da kuma jikkatar wasu 13, sakamakon tashin wutar lantarki a unguwar Tudun-Wada, Pantami a jihar.

Wutar ta tashi ne da safiyar ranar Asabar sakamakon matsala da ta taso daga wata tiransifoma a yankin, kamar yadda kakakin ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana.

Cikin waɗanda suka rasa rayukansu har da Babban Sakatare na Ma’aikatar Ayyuka ta Musamman ta jihar, Alhaji Muhammad Yusuf Kulani, tare da ’ya’yansa da wasu mazauna unguwar.

Marigayin shi ne shugaban ƙungiyar ƙwararrun akantoci ta Jihar Gombe (ANAN).

’Yan sanda daga ofishin Low-Cost sun isa wajen don tabbatar da tsaro da kuma kai waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Bello Yahaya, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan.

Ya kuma ce za su gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin tashin wutar da kuma ɗaukar matakan kare faruwar hakan a gaba.

Ya kuma roƙi al’umma da su kasance masu bin doka tare da bayar da haɗin kai yayin gudanar da binciken.