✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa mutum 3 hukuncin kisa kan kisan kai a Gombe

Shari’ar ta fara tun ranar 17 ga watan Nuwamba, 2022, kuma an kammala ta a ranar Laraba, 24 ga Yuli, 2025.

Babbar Kotun Jiha a Gombe mai lamba ta 3 ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu mutum uku bisa laifin haɗa baki da kuma kisan kai.

Alƙalin kotun Mai shari’a Haruna Kereng ne ya jagoranci shari’ar, inda ya ce kotu ta sami Dauda Mohammed Abubakar (wanda aka fi sani da Agenda) da Kabiru Abubakar (Gwarei) da Ibrahim Suleiman da laifi a kan dukkanin tuhume-tuhumen da ake musu dangane da kisan Ibrahim Yahaya a unguwar Herwagana da ke Ƙaramar Hukumar Gombe a ranar 22 ga Afrilu, 2022.

Kotun ta ji cewa, mutanen ukun sun kai wa Ibrahim Yahaya hari ɗauke da makamai masu haɗari kamar: takubba da wuƙa, inda suka kashe shi tare da jikkata wasu mutane biyu, wato Ahmed Abubakar da Muhammad Ahmed Lawan a lokacin harin.

Shari’ar ta fara tun ranar 17 ga watan Nuwamba, 2022, kuma an kammala ta a ranar Laraba, 24 ga Yuli, 2025.

Kereng ya bayyana cewa masu gabatar da ƙara sun gabatar da hujjoji masu ƙarfi da suka tabbatar da laifin da waɗanda ake tuhuma suka aikata, kamar yadda doka ta tanada a sashe na 97 da 221 na dokar laifuka, wanda ta tanadar da hukuncin kisa ga wanda aka same shi da laifin haɗa baki da kuma kisan kai.

Yayin da yake yanke hukunci, Mai sharia Kereng ya ce “Kowannen ku za a rataye shi a wuyansa har sai an tabbatar da mutuwarsa ta hanyar gwajin likita.”

Ya kara da cewa kotu ba ta da ikon rage hukuncin, don haka ba ta saurari roƙon sassauci ba.