✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya da iska sun rushe gidaje 171 a watanni biyu a Gombe – SEMA

Abdullahi Haruna Abdullahi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gombe, inda ya ce iftila’in ya shafi ƙananan hukumomin…

Hukumar Bayar da agajin gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA) ta bayyana cewa, ambaliya da iska mai ƙarfi sun rushe da lalata gidaje 171 a yankunan jihar cikin watanni biyu da suka gabata, lamarin da ya haddasa asara da kuma mutuwar yara huɗu.

Sakataren zartarwa na Hukumar SEMA, Malam Abdullahi Haruna Abdullahi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gombe, inda ya ce iftila’in ya shafi ƙananan hukumomin Dukku da Kwami da Gombe da Akko.

“Mun samu rahoton rushewar gidaje 87 a Dukku, 27 a Kwami, 30 a Gombe da kuma 27 a Akko, ciki har da wata coci da ambaliya ta lalata.

Haka kuma yara huɗu sun rasa rayukansu, mafi yawansu yara ne,” in ji shi.

Ya bayyana cewa, rashin tsaftar muhalli da kuma yawan sare bishiyoyi na daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen haddasa ibtila’in.

Ya yi kira ga al’umma da su daina zubar da shara a cikin magudanan ruwa, tare da amfani da wuraren zubar da shara da gwamnatin jihar ta gina.

“Akwai buƙatar kowa ya taka rawar gani wajen kare muhallinsa, musamman a lokacin damina.

Iyaye su kula da ‘ya’yansu, musamman ma yara ƙanana domin gudun afkuwar hatsarin faruwar hakan,” in ji Malam Abdullahi.

Sakataren SEMA ya kuma yi tir da yawan sare bishiyoyi domin yin gawayi na girki, yana mai cewa hakan yana ƙara haddasa fari da kuma rushewar muhalli.

Sai ya shawarci jama’a su ci gajiyar daminar da ake ciki wajen dasa bishiyoyi a gidajensu da unguwanninsu domin rage ƙarfi da haɗarin iska da kuma yaƙi da hamada.

Malam Abdullahi ya ƙara da cewa, Hukumar SEMA na shirin kai kayan tallafi ga waɗanda ibtila’in ya shafa a sassan jihar.