A ƙoƙarinta na bunƙasa noma da samar da isasshen abinci, Gwamnatin Jihar Gombe ta amince ta sayi tan 10,000 na taki, wanda ya yi daidai da buhu 200,000 domin shirin noman daminar bana.
Kwamishinan Harkokin Noma na Jihar, Dokta Barnabas Musa Malle, ya ce za a kashe Naira biliyan 8.8 wajen sayen takin.
- 1447: Yau ce ranar sabuwar shekarar Musulunci – Sarkin Musulmi
- 2027: Zan karɓi kowane irin muƙami da Tinubu zai ba ni — Sanata Barau
Ya ce hakan na nuna yadda gwamnatin jihar ke ƙoƙarin tallafa wa manoma da kuma ƙara samar da abinci a jihar.
Dokta Malle ya ce, “Gwamnati ta fito da sabbin hanyoyin aiki sama da yadda aka yi a baya, kuma za a raba wa manoma takin domin su fara amfani da shi kafin damina ta sauka.”
Ya kuma bayyana cewa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya zai ƙaddamar da wannan shiri a ranar Alhamis, 26 ga watan Yuni, 2025.
An shirya sayar da takin a farashi mai rahusa domin manoma su iya saya.
Wannan shiri yana daga cikin matakan gwamnatin na tabbatar da ci gaba a harkar noma da kuma shawo kan matsalar ƙarancin abinci a nan gaba.