Gwamnatin Jihar Sakkwato, ta bayyana cewa ta shirya zama da ’yan bindiga domin tattaunawa idan har suna da niyyar ajiye makamansu su rungumi zaman lafiya.
Wannan bayani ya fito ne daga Hadimi na Musamman kan Harkokin Tsaro na Gwamna Ahmed Aliyu, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya).
- Sojoji sun raunata shugaban ISWAP na Najeriya, Albarnawi
- Litar fetur za ta iya komawa N1,000 a Najeriya saboda yakin Isra’ila-Iran – Masana
Hadimin ya ce gwamnatin jihar na son tattaunawa don samar da zaman lafiya fiye da ci gaba da tafka yaƙi.
Gwamnatin ta ce a tarihi, an fi samu damar warware rikice-rikice da dama ta hanyar yin sulhu, ba ta hanyar amfani da ƙarfi kaɗai ba.
Saboda haka, jihar za ta iya tattaunawa da duk ’yan bindigar da suka yi niyyar miƙa wuya su dawo cikin al’umma lafiya.
Haka kuma, gwamnatin jihar ta nuna godiya ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, shugabannin rundunonin tsaro, da dukkanin jami’an tsaro da ke aiki wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
“Muna godiya matuƙa da sadaukarwarsu. Allah Ya jikan jarumanmu da suka rasu, ya bai wa iyalansu haƙuri,” in ji sanarwar.
Gwamnatin ta yaba da shirin da Gwamnatin Tarayya ke yi na tura masu gadi daji domin inganta tsaro.
Amma ta jaddada cewa dole ne a tabbatar da sahihanci da amincewar al’umma wajen ɗaukar aikin.
Ta kuma ce dole ne a sanya masu gadin daji su yi aiki ne ƙarƙashin kulawar hukumomin tsaro domin hana aikata ba daidai ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa dole ne a tabbatar da kyakkyawar sadarwa tsakanin masu gadin daji da al’umma.
Ta ce wannan zai taimaka wajen samar da amana da goyon baya daga mutanen da ake son karewa.
Hakazalika, Gwamnatin ta jaddada cewa tana da cikakken ƙudiri wajen samar da zaman lafiya da tsaro ga kowa.
Ta ce ba za ta tsaya ko ta yi ƙasa a guiwa ba wajen tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a faɗin jihar.
Wannan mataki yana nuna cewa gwamnat8i na son yin haɗin gwiwa da al’umma domin samar da dawwamammen zaman lafiya.