✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 147 a Gombe da Edo cikin Wata 6 — FRSC

Hukumar ta zayyano dilalan da ke yawan haddasa haɗuran.

Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta bayyana cewa mutum 147 ne suka rasu a sanadin hatsarin mota daban-daban a Jihohin Gombe da Edo tsakanin watan Janairu zuwa Yunin 2025.

A Jihar Gombe, kwamandan FRSC, Mista Samson Kaura, ya ce an samu haɗura 171 a tsakanin wannan lokaci.

Ya ce hatsari daban-daban ya rutsa da mutum 1,156.

Daga cikinsu, mutum 72 sun rasu, yayin da 641 suka jikkata, sai mutum 443 da ba su samu rauni ba.

Ya bayyana cewa motoci 234 ne hatsari ya rutsa da su, inda 105 daga cikinsu kekuna ne da kuma babur mai ƙafa uku.

Ya ce mafi yawan haɗuran sun faru ne sakamakon gudun wuce ƙima, tuƙin ganganci, da kuma ɗaukar mutane fiye da ƙima.

Mista Kaura, ya soki halayen wasu direbobi a yayin tuƙi a jihar, ya kuma shawarci direbobi su riƙa duba motocinsu kafin su hau hanya, musamman a lokacin damina.

A Jihar Edo kuwa, Kwamandan FRSC, Cyril Mathew, ya ce mutum 75 ne suka rasu a hatsarin mota 101 da suka faru cikin watanni shida.

Ya ce mutum 903 ne hatsarin ya rutsa da su, inda 304 daga cikinsu suka jikkata.

Ya bayyana cewa sanadin hatsarin ya haɗa da matsalar birki, gudun wuce gona da iri, tuƙin ganganci, amfani da waya yayin tuƙi, da kuma bin hannu ba daidai.

Mista Mathew, ya ce FRSC ta ƙara wayar da kan jama’a muhimmancin dokokin tuƙi cikin tsari.

Ya kuma ja kunnen direbobi su guji tuƙi yayin da suka sha giya, da guje wa tafiya cikin dare, lodin kaya fiye da ƙima, kuma su guji amfani da waya yayin tuƙi.