✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 21 sun rasu a hatsarin mota a kan hanyar Zariya–Kano

FRSC ta gargaɗi direbobi kan tuƙin ganganci.

Aƙalla mutum 21 ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Zariya zuwa Kano.

Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), reshen jihar ce ta tabbatar aukuwar hatsarin.

Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:23 na safe a unguwar Kasuwar Dogo da ke yankin Dakatsalle.

Hatsarin ya rutsa da wata babbar mota ƙirar DAF mai lambar GWL 422 ZE da kuma motar ɗaukar fasinjoji ƙirar Toyota Hummer mai lambar KMC 171 YM.

FRSC, ta ce bincike ya nuna cewa direban motar fasinjojin ne ya karya doka ta hanyar bin hanyar da ba ta dace ba, wanda hakan ya sa suka yi karo da babbar motar.

Bayan aukuwar hatsarin, motocin biyu sun kama da wuta, inda mutane da dama suka ƙone ƙurmus.

Kwamandan FRSC na Kano, MB Bature, ya ce jami’ansu sun isa wajen cikin gaggawa bayan samun rahoto.

Sun kuma kira ma’aikatan kashe gobara na jihar da na tarayya domin kashe gobarar da kuma ceto waɗanda hatsarin ya rutsa da su.

Mai magana da yawun FRSC, Abdullahi Labaran, ya ce: “Mutum 24 ne hatsarin ya rutsa da su. Abin takaici, 21 sun rasu, yayin da uku suka jikkata.”

Gawarwakin da suka ƙone an kai su ɗakin ajiye gawa na Asibitin Nassarawa da ke Kano, yayin da waɗanda suka jikkata ke samun kulawa a Asibitin Gwamnati da ke Garun Malam.

Bayan haka, jami’an FRSC tare da taimakon ’yan sanda sun ɗauke motocin da suka tare hanya domin sauƙaƙa zirga-zirgar ababen hawa a titin.

Kwamanda Bature, ya bayyana alhininsa kan wannan mummunan lamari, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu.

Ya kuma yi wa waɗanda suka jikkata addu’ar samun sauƙi.

Ya kuma yi amfani da wannan dama wajen jan hankalin direbobi su guji karya doka; kamar bin hanya ba daidai ba da tuƙin ganganci, wanda hakan ke haddasa haɗura.

“Wannan lamari abin takaici ne wanda ke nuna muhimmancin bin ƙa’idojin hanya. Mafi yawan haɗura za a iya kauce musu idan direbobi za su kiyaye doka,” in ji Bature.

Ya kuma buƙaci direbobi, musamman na motocin haya, da su guji gudu fiye da ƙima da ganganci a hanya, wanda a cewarsa shi ne babban dalilin da ke haddasa haɗura da asarar rayuka.

Ga hotunan yadda hatsarin ya auku: