An yi wa marigayi Alhaji Aminu Ɗantata jana’izar Salatul ‘Ga’ib’ a garin Kano.
An yi sallar ne a masallacin Umar bn Khattab da ke kan titin Gyadi-Gyadi.
- Za a binne Aminu Ɗantata a Madina — Iyalansa
- Mangu: Gwamnatin Filato ba ta aiko da wakilai don yin ta’aziyya ba — Sarkin Zazzau
Sheikh Ibrahim Khalil, Shugaban Majalisar Malamai na Jihar Kano, tare da Sheikh Ibrahim Aminu Daurawa, ne suka jagoranci sallar.
Manyan baƙi da dama sun halarci jana’izar, ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, mambobin majalisar zartarwa na Jihar Kano, manyan ‘yan kasuwa da wasu mutane.
Aminiya ta ruwaito marigayi Alhaji Aminu Dantata, ya rasu a birnin Abu Dhabi, kuma za a birne shi a Madina bayan wasiyyar da ya bari kafin rasuwarsa.
Ga hotunan a ƙasa: