✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a binne Aminu Ɗantata a Madina — Iyalansa

Marigayin ya bar wasiyyar cewar idan ya rasu a birne shi a Birnin Madina na Ƙasar Saudiyya.

Iyalan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata, wanda ya rasu, sun bayyana cewa ya bar wasiyyar cewa a birne shi a Birnin Madina na ƙasar Saudiyya.

Majiyoyi daga cikin iyalansa sun bayyana cewa marigayin ya buƙaci a birne shi kusa da uwargidansa a Madina a duk lokacin da ya rasu.

A gefe guda kuma, Majalisar Malamai ta Jihar Kano ta yi wa marigayin sallar Ga’ib a Masallacin Aliyu bin Abu Talib da ke unguwar Dangi.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, majalisar ta bayyana cewa za a yi masa sallar ne duk d gawarsa na Birnin Dubai, na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

An gudanar da sallar a cikin birnin Kano, da misalin ƙarfe 2 na rana.

Sanarwar ta buƙaci al’umma da su halarta domin yin sallar da kuma yi wa marigayin addu’o’i.

Alhaji Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekaru 94 bayan fama da rashin lafiya.

Ya rasu yana da ’ya’ya bakwai da jikoki da dama.

Babban sakatarensa, Mustapha Abdullahi Junaid, ne ya sanar da rasuwar a safiyar Asabar.

Ɗaya daga cikin attajirai mafiya arziƙi a Nahiyar Afirka, ya rasu ne a ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE.)

Alhaji Aminu Ɗantata shi ne mai kamfanin mai na Express Petroleum & Gas, kuma a matsayin uba yake ga attajirin Afirka, Alhaji Aliko Ɗangote.