✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun ƙoli ta tabbatar da Okpebholo a matsayin gwamnan Edo

Wannan hukunci ya kawo ƙarshen duk wata shari’a da ta shafi zaɓen Gwamnan Jihar Edo,

Kotun Ƙoli ta tabbatar da Sanata Monday Okpebholo na jam’iyyar APC a matsayin sahihin Gwamnan Jihar Edo.

Wannan hukunci ya kawo ƙarshen shari’ar da ake yi biyo bayan zaɓen gwamnan jihar da aka yi a ranar 21 ga watan Satumba, 2024.

Kwamitin alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Garba ne, suka yanke hukuncin a ranar Alhamis.

Sun yi watsi da ƙarar da ɗan takarar PDP, Asue Ighodalo, ya shigar, kan cewar hujjojin da ya gabatar ba su da inganci.

Mai Shari’a Garba, ya ce Ighodalo da jam’iyyarsa PDP ba su kawo hujjoji masu ƙarfi da za su nuna cewa Okpebholo bai lashe zaɓen bisa ƙa’ida ba.

Ya kuma ƙara da cewa PDP ba ta bayyana yadda hukuncin kotun ƙasa da kotun ɗaukaka ƙara suka saɓa doka ba.

Tun da farko, PDP ta ce an samu matsaloli da kura-kurai a lokacin zaɓen, kuma ta nemi kotu ta soke sakamakon.

Amma kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara sun yi watsi da ƙarar.

Hakan ne ya sa suka garzaya Kotun Ƙoli don neman haƙƙinsu.

Wannan hukunci na yau Alhamis, ya kawo ƙarshen duk wata shari’a da ta shafi zaɓen Gwamnan Jihar Edo, kuma Okpebholo zai ci gaba da zama gwamnan jihar.