Hadimin Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, kan Harkokin Yaɗa Labarai, Temitope Ajayi, ya mayar wa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha martani, kan cewa Tinubu bai taimaka wa tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ba wajen zama shugaban ƙasa a 2015.
Ajayi, ya ce Buhari yana da ƙarfi sosai a Arewa amma hakan bai hana shi faɗuwa zaɓukan 2003, 2007 da 2011 ba.
- Isra’ila ta kashe Falasdinawa 24 a Zirin Gaza
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata
Ya bayyana cewa a zaɓen fidda gwanin jam’iyyar APC da aka yi a 2014, Tinubu ne, ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin Buhari ya lashe.
Ya ce Tinubu ne ya shawo kan gwamnonin APC da wakilan Kudu maso Yamma su mara wa Buhari baya a lokacin zaɓen da aka yi a filin wasa na Teslim Balogun a Legas.
Ya ce ba don wannan goyon baya ba, da Buhari bai samu tikitin takarar shugaban ƙasa ba.
Ajayi, ya ce bai dace a raina ƙoƙarin Tinubu da sauran waɗanda suka taimaka wa Buhari ba.
Ya ce Boss Mustapha bai faɗi gaskiyar abin da ya faru ba.
“Mu bar maganar babban zaɓen da Buhari ya lashe. Ai da bai zama ɗan takara a jam’iyyar APC ba, da ba zai taɓa zama shugaban ƙasa ba.
“Kuma da babu goyon bayan Tinubu a zaɓen fidda gwanin APC da aka yi a Legas a 2014, da Buhari bai lashe ba.”