Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya ce ba Shugaban Kasa Bola Tinubu kaɗi ne ya sa Muhammadu Buhari ya ci zabensa a shekarar 2015 ba.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a Abuja ranar Laraba, yayin kaddamar da littafin da mai magana da yawun tsohon Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya wallafa kan abubuwan da ya gani a zamanin mulkinsu.
Buhari dai ya shugabanci Najeriya ne daga shekarar 2015 zuwa 2023.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Neja
- Ana zargin takalar faɗa tsakanin fadar Aminu Ado da Sanusi II
Daga cikin manyan bakin da suka halarci kaddamar da littafin akwai tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Yakubu Gowon da tsohon Mataimakan Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da Yemi Osinbajo da Sakataren Gwamnatin Tarayya mai ci, George Akume da dai sauransu.
Idan za a iya tunawa, yayin wani taron neman goyon bayan wakilan jam’iyyar APC a jihar Ogun a aranar daya ga watan Yunin 2022 gabanin zaben fi-da-gwani na jam’iyyar, Tinubu ya yi ikirarin cewa da ba dan shi ba, da Buhari bai ci zaben 2015 ba.
To sai dai da yake gabatar da mukala a kan nasarorin mulkin Buhari, Boss ya ce akwai jiga-jigan APC da dama da suka taimaka aka sami nasarar, ba wai Tinubu shi kadai ba, yana mai cewa gaskiya da rikon amanar Buharin ma sun taka rawa.
Ya ce, “Akwai kuma bangarorin jam’iyyar CPC ita kanta, akwai na ANPP da na ACN da APGA da kuma wani tsagi na PDP da ya balle ya shigo cikin hadakar APC. Tinubu ya taka rawar gani, sannan Sanata Ali Modu Sheriff wanda tsohon Shugaban Kwamitin Amintattu ne na ANPP shi ma ya yi kokari.
“Hadakar ta yi nasarar kafa tarihin farko a Najeriya inda aka kayar da shugaba mai ci, kuma gaskiya da rikon amanar shi su ne a kan gaba wajen samun wannan nasarar.
“A bangarenmu na ACN, ba na so na tayar da kura, amma makasudin hada majar ita ce don a tsayar da Buhari takara saboda mun kalli alkaluman kuri’unsa na baya.
“A shekara ta 2003, an fafata tsakanin Buhari da Obasanjo, inda Buharin ya sami kuri’a miliyan 2.7. A 2007 kuma, ya sami miliyan 6.6, sai a 2011 kuma ta karu zuwa 12.2.
“Lokacin da muka kokarin hada APC, jam’iyyar CPC ta Buhari na da Gwamna daya, ACN na da shida, sai ANPP na da uku. Idan ka hada jimlar kuri’un da muka samu a zaben Shugaban Kasa a 2015 kuma miliyan 15.4 ne.
“Ka ga ke nan kuri’un da muka kara wa Buhari bayan kafa APC a kan kuri’u miliyan 12.5 din da Buhari ya zo da su daga CPC su ne miliyan uku,” in ji Boss Mustapha.