✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwanan nan gwamnati za ta sake kara kudin lantarki a Najeriya – Minista

Ministan Lantarki na Najeriya, Adebayo Adelabu, ya ce Gwamnatin Tarayya na shirye-shiryen sake kara kudin wutar lantarki domin rage yawan bashin da bangaren lantarkin ke…

Ministan Lantarki na Najeriya, Adebayo Adelabu, ya ce Gwamnatin Tarayya na shirye-shiryen sake kara kudin wutar lantarki domin rage yawan bashin da bangaren lantarkin ke bi.

Bayanai dai sun nuna yanzu haka, bashin lantarkin da ake bi a Najeriya ya haura Naira tiriliyan hudu.

Amma a cewar ministan a yayin wani taron masu ruwa da tsaki 300 a Abuja, yunkurin wani bangare ne na tabbatar da cewa bangaren lantarki ya tsaya da kafarsa.

Idan dai za a iya tunawa, duk da Karin kudin wutar da aka yi wa kwastomomin da ke tsarin Band A, mutane na ci gaba da korafin cewa ba sa samun isasshiyar wutar da ta kai ta kimar abin da suke biya.

Sai dai ministan ya ce yin karin na da muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya da kuma ci gaban kasa.

A cewarsa, “A yanzu haka, akwai tarin bashin da lamfanonin da ke samar da wutar ke bin bashi sakamakon cire tallafin lantarkin da gwamnatin ta yi, wanda yah aura Naira tiriliyan hudu a karshen watan Disambar bara.

“Tuni gwamnatin ta fara tsare-tsaren ganin cewa wannan bashin bai ci gaba da taruwa ba, shi ya sa ma take kokarin kara farashin wutar, sannan ta kirkiro da sabon tallafi ga masu karamin karfi a cikin masu amfani da wutar.

“Abin da hakan ke nufi shi ne gwamnati za ta kawo karshen tallafin da take biya, wanda hakan ke nufin za a sami karuwar farashin a dukkan matakai,” in ji Ministan.