Wani bincike da Cibiyar Bincike ta Africa Polling Institute (API), ta gudanar ya nuna cewa yawancin ’yan Najeriya ba su da ƙwarin gwiwa game da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Majalisar Dokoki da kuma ɓangaren shari’a.
An bayyana sakamakon Binciken Haɗin Kan Al’ummar Najeriya na 2025, a wani taron ƙasa da aka gudanar a Abuja.
- Elon Musk zai kafa sabuwar jam’iyyar siyasa a Amurka
- Tinubu ya umarci sojoji su murƙushe ’yan ta’adda a faɗin Najeriya
Bincike ya nuna kashi 83 cikin 100 na ’yan Najeriya ba su yadda da Gwamnatin Tarayya da Shugaba Tinubu ke jagoranta ba.
Haka kuma, kashi 82 cikin 100 ba su da ƙwarin gwiwa kan Majalisar Dokoki, wadda ke ƙarƙashin jagorancin Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen.
Ɓangaren shari’a, wanda Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun ke jagoranta, ya nuna kashi 79 cikin 100 na mutane sun ce ba su yadda da sahihanci shari’a a ƙasar ba.
Rahoton ya nuna cewa Ma’aunin Haɗin Kan Al’umma a Najeriya ya tsaya a kashi 46.8 cikin 100, ƙasa da matsakaicin kashi 50 da ake buƙata ƙasa ta samu.
Wannan na nufin akwai matsaloli da dama da suka shafi rashin haɗin kai, rashin yadda da juna da rashin jin-ƙai a matsayin ’yan ƙasa ɗaya.
Darakta Janar na API, Farfesa Bell Ihua, ya bayyana cewa wannan shi ne mafi munin bincike wajen amincewa da gwamnati tun da suka fara gudanar da irin wannan bincike a shekarar 2019.
An gudanar da binciken ne daga watan Janairu zuwa Fabrairun 2025, inda aka zanta da mutum 5,465 a faɗin Najeriya.
An yi tambayoyin cikin harsunan gida irin su Hausa, Yarabanci, Igbo da Pidgin.
Binciken ya mayar da hankali kan ra’ayoyin jama’a game da abubuwa 14, kamar su yadda mutane ke kallon kansu, yadda suka yadda da gwamnati, shiga harkokin ƙasa, cin hanci, daidaito tsakanin jinsi da makomar ƙasar.
Matsin rayuwa ya haɗa kan ’yan Najeriya
Wahalhalun rayuwa sun haɗa kan jama’a a Najeriya, sai dai an samu rarrabuwar kai ta fuskar siyasa da ƙabilanci, amma mafi yawan ’yan Najeriya sun haɗu ne ta fuskar abin da ya shafi matsalar rayuwa.
Mutane da dama sun bayyana cewa suna fama da tsadar rayuwa musamman farashin abinci, sufuri da sauran abubuwan more rayuwa a ƙarƙashin abin da ake kira “Tattalin Arziƙin Tinubu”.
Rahoton ya ce kashi 53 cikin 100 na ’yan Najeriya sun ce suna takaicin yadda abubuwa suke a ƙasar, yayin da kashi 33 cikin 100 kacal ke alfahari da zama ’yan Najeriya.
Kashi 11 cikin 100 ne kacal suka nuna jin daɗin kasancewar ’yan Najeriya.
Rashin yadda da gwamnati da cin hanci
Duk da fargaba da rashin jin daɗin halin da ƙasar ke ciki, yawancin ’yan Najeriya har yanzu na yi mata fatan alheri.
Sakamakon binciken ya nuna cewa mutane da yawa na son shiga harkokin siyasa domin kawo canji.
Mutane da dama na goyon bayan auren juna tsakanin ƙabilu da addinai daban-daban domin samun haɗin kai.
Amma cin hanci da rashawa na ƙara ƙarfi. Mutum shida daga cikin 10 da aka tambaya sun ce cin hanci ya ƙaru cikin shekara guda.
Kashi 64 cikin 100 kuma sun ce gwamnati ba ta yin aiki yadda ya kamata wajen yaƙi da cin hanci.
Daidaiton jinsi da jagoranci
Game da batun daidaito tsakanin mata da maza, kashi 71 cikin 100 sun yadda cewa mata su ma za su iya riƙe madafun iko kamar maza.
Kashi 63 cikin 100 ma sun ce da za su samu dama za su kaɗa wa mata ƙuri’a domin zama shugabar ƙasa.
Amma kashi 39 cikin 100 kawai ke ganin cewa gwamnati na yin ƙoƙari wajen ganin an samu daidaito tsakanin jinsi.
Yi wa Najeriya fatan alheri
Duk da matsin rayuwa, kashi 56 cikin 100 na mutane suna yi wa Najeriya fatan alheri da burin ganin ta inganta.
Har ila yau, kashi 53 cikin 100 sun ce da za su samu dama, za su bar ƙasar tare da iyalansu. Yayin kashi 59 cikin 100 kuma sun ce ba sa jin daɗin irin rayuwar da suke yi yanzu.
Shawarar cibiyar API ga gwamnati
Cibiyar API ta bayar da shawarar cewa gwamnati ta kafa Hukumar Haɗin Kan Ƙasa wadda za ta kula da tsare-tsaren da za su taimaka wajen ɗinke ɓarakar da ke tsakanin ’yan ƙasa da kuma wanzar da amincewa da gwamnati.
Sannan ta ce gwamnati ta tabbatar da irin alƙawuran da take yi wa ’yan ƙasa, abin da ake kira yarjejeniya tsakanin gwamnati da al’umma domin kawo ƙarshen irin wannan rashin yadda.
Haka kuma, an buƙaci hukumomi irin su Hukumar Wayar da Kan Jama’a (NOA), Ma’aikatar Yaɗa Labarai, da Gidan Talabijin na (NTA( da su watsa shirye-shiryen da ke ƙarfafa haɗin kan al’umma da jin-ƙai.
Farfesa Ihua, ya jaddada rawar da ƙungiyoyin fararen hula za su iya takawa wajen dawo da amincewa, zaman lafiya da haɗin kai, wanda ya ce dole ne ’yan Najeriya su shiga harkokin al’umma da tattaunawa don samar da makoma ga ƙasar.
Wannan rahoton shi ne na huɗu da API ta fitar a jerin rahotanninta kan haɗin kai, bayan na shekarun 2019, 2021 da kuma 2022.