’Yan sanda sun kama wani matashi mai mai shekara 24 kan zargin ya kashe mahaifinsa mai shekaru 70 a ƙauyen Uzum da ke Ƙaramar Hukumar Giade ta jihar Bauchi.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce matashin ya yi amfani da sanda ne ya bugi mahaifin nasa a kai, nan take dattijon ya faɗi ya mutu.
Wani mazaunin ƙauyen Uzum da ke Giaɗe ya ce ake zargin ya lakaɗa wa mahaifinsa duka ne da sanda yayin da suke taƙaddama a gida da misalin karfe 10:30 na daren ranar Alhamis din da ta gabata.
Ya ce, “Ba mu san abin da ya faru ba, amma dai mun ji wata babbar hayaniya tsakaninsu, lamarin da ya sa shi ya bugi mahaifinsa da sanda a kai, mahaifin ya faɗi a sume.
- Mai shekara 70 ya kashe ƙanwarsa kan gadon gona a Jigawa
- Gwamnan Bauchi ya ƙaddamar da kwamitin ƙirƙiro da sabbin masarautu
“Mun sanar da ’yan sanda suka zo suka kai shi Babban Asibitin da ke Giaɗe, inda wani likita ya tabbatar da rasuwarsa da isar sa asibitin.”
Wakil ya bayyana wa manema labarai a ranar Juma’a a Bauchi cewa a ranar Alhamis da dare ne wani mutumin kirki ya kira su a ranar ya sanar da su.
Ya ce, “Da samun labarin kwamishinan ’yan sandan jihar Sani Omolori ya umurci jami’in ’yan sanda (DPO) da ke kula da Ofishin Shiyyar Giaɗe da ya gudanar da bincike domin gano ainihin abin da ya faru.
“Jami’an ’yan sanda sun je wurin da lamarin ya faru inda suka sami marigayin a kwance jina-jina, suka kai Babban Asibitin Giaɗe kuma likitan ya tabbatar da cewa ya rasu. An kuma miƙa gawarsa ga iyalansa domin yin jana’izarsa kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada.”
Ya ci gaba da cewa rundunar tana ci gaba da gudanar da bincike, babban wanda ake zargin kuma yana hannun ’yan sanda kuma bayan an kammala bincike za a gurfanar da shi a gaban kotu.