Rundunar ’sanda ta jihar Delta ta ja kunnen matasan jihar a kan yin shigar banza, inda ta ce duk wanda aka kama za a iya cin shi tarar da ta kai ta naira 50,000.
A cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar a jihar, SP Bright Edafe ya fitar ranar Talata, ya ce yin shigar banzan ya saba da dokar hana cin zarafin mutane ta (VAPP).
- Ko ɗaya Buhari bai yi wa takarar Tinubu zagon ƙasa ba – Garba Shehu
- Za mu shige gaba idan aka dawo da tattauna shirin nukiliyar Iran — EU
Kazalika sanarwar ’yan sandan ta nuna bacin rai game da shigar banza da matasa a jihar suka runguma.
“Akwai wasu daga cikin dokokin da aka kafa da mafi mutanene suka San dasu ba to Amma zamu riqa fito dasu xaya bayan xaya don a sani.
“Duk wata shiga da ke nuna tsiraicin mutum a fakaice za a ci tarar duk wanda aka kama da laifi. Gwamnatin Jihar Delta ba da wasa take ba, sannan ba ta kafa wadannan dokokin don wasa ba,” in ji sanarwar ’yan sandan.
An samar da kuma kafa dokar VAPP a shekara ta 2015 lokacin tsohon shugaban Kasa Goodluck Jonathan, kuma jihar Delta ma ta amince da dokar.
Rundunar ta ce ba iya shigar banza ba, dokar ta ku8ma hana yi wa ’ya’ya mata kaciya da cin zarafin yara marayu.