✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe ɗan sanda, sun jikkata wasu 3 a Zariya

Maharan sun yi musayar wuta da 'yan sandan kafin su kashe ɗaya daga cikinsu.

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai wa motar ’yan sanda hari a Zariya, inda suka harbe ɗaya daga cikinsu har lahira, tare da raunata wasu uku.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Talata, a unguwar Dalan Waje da ke kan hanyar Galadimawa, a Ƙaramar Hukumar Zariya da ke Jihar Kaduna.

A cewar wani mazaunin yankin da ya shaida faruwar lamarin, motar ‘yan sandan na bin wata mota ƙirar Golf kafin a ji ƙarar harbe-harbe.

Nan take mutane suka fara kwanciya a ƙasa domin tsira da rayukansu.

Wannan hari ya girgiza mazauna yankin, inda suka ce ko da yake yankin ya daɗe yana fama da hare-haren ’yan bindiga, amma an daɗe ba samu hari ba.

A harin, an kashe wani ɗan sanda mai suna Nasiru Musa.

Ɗan sandan mazaunin ƙofar Kibo ne a cikin birnin Zariya.

Sauran da suka jikkata sun haɗa da direban motar ’yan sandan, Auwalu Hassan Ɗan Jos, wani ɗan-sa-kai mai suna Awwal Hassan, Iliyasu Ya’u da Salisu Mohammed.

An garzaya da su zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya, domin samun kulawar likitoci.

Da Aminiya ta tuntuɓi kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansur Hassan, ya ce yana wajen wani taron sanin makamar aiki, don haka bai da cikakken bayani.