Mahaifin ango da ƙanin ango na daga cikin mutanen da aka kashe lokacin da wasu suka kai musu hari a Jihar Filato.
Rahotanni sun nuna cewa mutum 31 ne ke cikin wata babbar mota mai ɗaukar fasinja 18 daga Jami’ar Ahmadu Bello Zariya (ABU), yayin da aka kai musu hari.
- Ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe mutum 10 da bam a Borno
- An yi wa ma’aikatan ƙananan hukumomin Gombe ƙarin albashin N5,000
Mutanen sun fito ne daga unguwar Basawa da ke Ƙaramar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin Pau da ke Jihar Filato domin ɗaurin aure.
Mutum 12 sun rasu a sakamakon harin, yayin da 19 suka jikkata kuma ana kula da su a Asibitin Gwamnati na Mangu.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira, Ibrahim Umar, ya ce: “Mahaifi da ƙanin ango duk sun rasu a harin.
“Angon daga Zariya yake, amma yana aiki a matsayin malami a wata makaranta a yankin. A nan ne ya haɗu da matar da zai aura.
“Muna ɗauke da goro da sauran kayayyakin da ake kai wa wajen aure. Mun shaida wa waɗanda suka tare mu cewa ba ‘yan yankin ba ne, kuma mu ba ma faɗa, sai dai ba su saurare mu ba,” in ji shi.
Ya yaba da yadda sojojin da ke kusa da wajen suka kai musu ɗauki.
“Sojojin sun taimaka mana sosai. Da ba su zo ba, da abin ya fi haka muni,” in ji shi.