✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bam ya kashe mutum 5, 15 sun jikkata a Kano

Yanzu haka jami'an tsaro na ci gaba da bincike kan lamarin.

Aƙalla mutum biyar ne aka tabbatar da rasuwarsu, yayin da wasu 15 suka jikkata sakamakon fashewar wani bam a Jihar Kano.

Aminiya ta gano yadda fashewar bam ɗin ya haddasa firgici a yankin da lamarin ya faru, inda jami’an tsaro da na agajin gaggawa suka garzaya wajen don kai ɗauki.

Lamarin ya faru a ranar Asabar, a unguwar Hotoro Eastern Bypass kusa da wani kamfanin ƙarafa.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce fashewar na iya kasancewa bam ɗin da sojoji suke yin jigilar ne wanda aka yi sakaci ya fashe.

“Na samu kiran gaggawa cewa wani abu mai tayar da hankali ya faru. Da na isa wajen, sai na ga abin kamar bama-baman sojoji ne suka fashe.

“Mutane 15 sun jikkata, kuma abin takaici, guda biyar sun rasu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitocin da ke kusa yankin domin samun kulawa ta gaggawa.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa wata babbar mota ce ɗauke da kayan fashewar, wadda ta ke kan hanyar zuwa Jihar Yobe.

Har yanzu jami’an tsaro ba su tabbatar da ko motar sojoji ce ke ɗauke da kayan fashewar ba.

Rundunar na ci gaba da da bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin da kuma abin da ya haddasa fashewar abun.

“Za mu samu cikakken bayani bayan kammala bincike,” in ji Kwamishinan.

Ya kuma roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu.

Ga hotunan yadda jami’an tsaro ke bincike a wajen: