✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani ya kashe mahaifiyarsa mai shekara 71 a Akwa Ibom

An kama wanda ake zargin Alexander ne a ranar 10 ga watan Yuni, kuma a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike don…

Rundunar ’yan sandan Jihar Akwa Ibom ta kama wani mutum mai suna Alexander Peter bisa zarginsa da kashe mahaifiyarsa mai suna Madam Atiny Peter mai shekara 71 da adda.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Ikot Inyang da ke ƙaramar hukumar Oruk Anam a Jihar Akwa Ibom.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Baba Mohammed Azare ne ya tabbatar da kamen a yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis, a hedikwatar ’yan sanda da ke Ikot Akpan Abia, a Uyo.

Kwamishinan ’yan sandan ya bayyana cewa, an kama wanda ake zargin Alexander ne a ranar 10 ga watan Yuni, kuma a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin wannan ɗanyen aikin.

“Mummunan lamarin ya faru ne a ƙauyen Ikot Inyang da ke ƙaramar hukumar Oruk Anam, inda rahotanni suka ce wanda ake zargin ya yi amfani da adda ne wajen yi wa mahaifiyarsa kisan gillar,” in ji Kwamishinan, inda ya ce rundunar ’yan sandan na ƙoƙarin bankaɗo lamarin tare da gano musabbabin wannan aika-aika.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, an kama mutane 54 da ake zargi a faɗin jihar a cikin makonni shidan da suka gabata bisa aikata laifuka daban-daban.

Bugu da ƙari, rundunar ta ƙwato makamai da alburusai sama da 50 a wannan lokacin.

Kisan ya haifar da damuwa a cikin al’ummar yankin, inda mazauna yankin suka kaɗu matuƙa game da kisan da ɗan tsohuwar ya yi wa mahaifiyarsa da hannunsa.

‘Yan sanda sun ce za a samu ƙarin bayani yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.