✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ɗaure mutum 7 kan yi wa ɗan sanda rauni a Kano

Kotun ta kuma zartar musu da hukuncin share magudanan ruwan unguwanninsu.

Wata kotun shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Jihar Kano, ta yanke wa wasu mutum bakwai hukuncin ɗauri, bayan da suka ji wa wani ɗan sanda rauni yayin da ake ƙoƙarin cafke su.

Al’ummar unguwannin Tudun Maliki da Sheka ne suka kai rahoton mutanen, inda suka zarge su da sayar da miyagun ƙwayoyi.

A kotun, an gurfanar da su kan laifukan haɗa baki domin tayar da hankali, jikkata mutum, hana ‘yan sanda yin aikinsu yadda ya dace, da kuma ɓoye wanda ake zargi.

Lauyan gwamnati, Barrista Aliya Ibrahim Aminu ce, ta karanta musu tuhumar a gaban kotu.

Ɗaya daga cikinsu ya musanta laifin, yayin da Idris Ado da wasu mutum biyar suka amsa wasu daga cikin tuhumar amma suka ƙi amincewa da sauran.

Alƙalin kotun, Khadi Shamsuddeen Ado Abdullahi Unguwar Gini, ya yanke musu hukuncin ɗaurin wata uku bisa laifin farko, da wata uku a laifi na biyu.

Haka kuma ya ƙara yanke musu hukuncin ɗaurin wata uku tare da tarar Naira 15,000.

Za a yi wa kowannensu bulala 20.

Baya ga haka kuma, kotun ta umarce su da su yi wata shida a ƙarƙashin kulawa, inda za su riƙa share magudanan ruwa a unguwanninsu.