✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda wani ɗan sanda ya rasu a hanyar zuwa ɗaurin aurensa

SP Gumau ya rasu ne da misalin ƙarfe 9 yayin da ake shirin ɗaura masa aure da misalin ƙarfe 10.

Wani jami’in ɗan sanda, SP Mustapha Garba Gumau, ya yi gamo da ajalinsa a wani hatsarin mota yayin da ya rage aƙalla sa’a ɗaya a ɗaura masa aure.

Aminiya ta ruwaito cewa, ajali ya katse hanzarin jami’in ne a kan hanyar Gumau zuwa Magaman-Gumau da ke Ƙaramar Hukumar Toro ta Jihar Bauchi, inda za a ɗaura masa aure.

SP Gumau wanda hatsarin ya rutsa da shi da abokansa ya rasu ne da misalin ƙarfe 9 yayin da ake shirin ɗaura masa aure da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Asabar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Bauchi, CSP Mohammed Ahmed Wakil ya fitar ta ce an tabbatar da rasuwar matashin da ke shirin angwancewa bayan an garzaya da shi asibiti.

Wakil ya ce jami’in ya rasu tare da wasu abokansa biyu da ke cikin wata mota ƙirar marsandi bayan sun yi karo da wata motar ƙirar Opel Vectra.

Sanarwar ta ambato Kwamishinan ’yan sandan Bauchi, CP Auwal Sani Omolori yana jajanta wa iyalan mamatan da kuma addu’ar mutuwa ta zamanto hutu a gare su.