✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kira ga Haƙuri: A Dakatar da Ƙirƙirar Sabbin Masarautu a Jihar Bauchi

A bar kotu ta yanke hukunci. A bar zaman lafiya ya ɗore.

Saboda matsin lamba na doka da kuma la’akari da mahimman batutuwan siyasa, ya zama dole Gwamnatin Jihar Bauchi ta dakatar da duk wani ci gaba na aikin kwamitin da aka kafa a ranar 4 ga Yuli 2025 domin duba yiwuwar ƙirƙirar sabbin masarautu ko sauye-sauye ga tsarin majalisun gargajiya—musamman a yankunan da har yanzu ke fuskantar shari’a a kotu.

Ci gaba da wannan lamari mai sarkakiya alhali wasu muhimman ƙarar shari’a na ci gaba a kotuna, ba wai kawai zai saɓa wa kundin tsarin mulki da ikon shari’a ba, har ila yau, zai iya haddasa tayar da jijiyoyin wuya a cikin al’umma, musamman a yankunan da ke da tarihi na rikice-rikicen ƙabilanci kamar Tafawa Balewa da kewaye.

Wannan kira na haƙuri yana da tushe duka a doka da alhaki domin kare zaman lafiya da mutunta doka.

Shari’o’in da ke Gaban Kotu:

A bayyane yake cewa akwai manyan shari’o’i guda biyu da har yanzu ba a yanke hukunci kansu ba a Babbar Kotun Shari’a ta Jihar Bauchi, kuma akwai yiwuwar ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Jos:

Shari’o’in biyu sun haɗa da mai lamba: BA/191/2011 da ke gudana tsakanin Hon. Barr. Bukata Zhyadi da wasu 3 a ɓangare ɗaya, sai kuma Gwamnan Jihar Bauchi da wasu 15 a ɗaya ɓangaren.

Akwai kuma shari’a mai lamba: BA/173/2012 – wadda ake yi tsakanin Alhaji Maigida Abdullahi (Sarkin Tafawa Balewa) da wasu 4 a ɓangare ɗaya, da kuma Baba Garba Vurmi da wasu 7 a ɗaya ɓangaren.

Waɗannan shari’o’in suna da tushe a cikin dogon tarihin rikice-rikicen ƙabilanci a Tafawa Balewa, wanda tun daga 1959 ake fama da tarzoma lokaci zuwa lokaci, wanda ya haddasa salwantar rayuka da dukiya, sakamakon saɓani kan masarautun gargajiya, iyakokin ƙabilu da matsalolin ganewa tsakanin al’umma.

Ka’idar Haramta Tsoma Baki a Shari’ar Da ke Gaban Kotu:

Dangane da ka’idar (sub judice) wadda ta haramta tsoma baki a shari’ar da ke gaban kotu da kuma tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (wanda aka gyara), musamman sashe na 6(6)(b) — wanda ya ba da cikakken ikon yanke hukunci ga kotuna kawai.

Sai sashe na 14(2)(b) — wanda ya bayyana tsaron lafiya da walwalar jama’a a matsayin babban dalilin kafa gwamnati,

Ya zama rashin ɗa’a a doka, rashin adalci a akhlaƙi, da kuma sakaci a siyasa, a ci gaba da wani aiki na gwamnati ko na dokar majalisa wanda zai iya kawo cikas ga hukuncin da kotu take jira.

Bugu da ƙari, Kotun Koli ta Najeriya a hukuncinta na Gwamnan Legas a zamanin mulkin soji da kuma Ojukwu (1986) 1 NWLR (Pt. 18) 621, ta tabbatar da cewa babu wani ɓangare, har da gwamnati, da ya dace ya ɗauki mataki kai-tsaye a kan batutuwan da ke gaban kotu, domin hakan na raina ikon kotu da tsarin doka.

Ƙirƙirar sabbin masarautu ko ɗaukar matakin dokoki masu sarkakiya a yankunan da ake rigima da su, na iya sake tayar da tarzoma, karya zaman lafiya da rushe ƙoƙarin da aka daɗe ana yi na sasanta rigingimu a Kudancin Bauchi.

Shawarwari:

i) Gwamnatin Jihar Bauchi, Majalisar Zartarwa da Majalisar Dokoki su dakatar da duk wani tunani ko mataki kan ƙirƙirar sabbin masarautu ko sauya tsarin majalisun gargajiya a yankunan da abin ya shafa;

ii) Hukumomin tsaro da ƙungiyoyin wanzar da zaman lafiya su kasance cikin shiri da lura da duk wani yunƙuri da zai iya haddasa rikici a cikin al’umma;

iii) Sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin al’umma da dattawan yankuna su tallafa wa bin doka da tafiyar da mulki bisa zaman lafiya.

Kammalawa:

Gwamnatin Jihar Bauchi ya kamata ta tuna cewa matakin da aka ɗauka cikin gaggawa ko wulaƙanta tsarin shari’a, na iya fuskantar soke daga kotu, kuma illar hakan ga rayukan al’umma da hadin kai na jama’a ba za a iya aunawa ba.

A bar kotu ta yanke hukunci. A bar zaman lafiya ya ɗore.

Saƙo daga Mukhtar Abubakar Tafawa Balewa Bauchi, Najeriya