A ranar Litinin ɗin nan aka wayi gari da fastocin takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027 na Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed.
An liƙa fastocin wuri-wuri da suka haɗa da shataletale da turakun wutar lantarki da allunan tallace-tallace daban-daban a wasu manyan tituna da ke ƙwaryar birnin na Bauchi.
- HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa da matsalar tsaro a Filato
- Bikin Ista: Hatsarin mota ya laƙume rayuka 5 a Gombe
Aminiya ta ruwaito cewa fastocin masu ɗauke da saƙon “Kaura for President” an manna su a wasu manyan hanyoyi da suka haɗa da titin jirgin ƙasa, Sabon Titin Karofi da kuma Ƙofar Dumi.
Ɗaya daga cikin matasan da ke aikin manna fastocin, Aminu Auwal, ya shaida wa Aminiya cewa wasu ’yan siyasa biyu — Ya’u Ortega da Talolo — ne suka ba su kwangilar.
Auwal ya ce: “an ba mu kwangilar liƙa fastocin gwamnan a manyan hanyoyi da ke cikin birnin Bauchi.
“Tun wurin ƙarfe 1:00 na dare muka fara wannan aiki kuma muna sa ran kammalawa a yau [Litinin].”
Sai dai ƙoƙarin jin ta bakin ’yan siyasar biyu da suka ba da wannan kwangilar ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.