Mahara sun sake kai hari tare da kashe akalla mutum 17 a kananan hukumomin Mangu da Bokkos na jihar Filato.
Rahotanni sun nuna an kai harin ne ranar Alhamis a kauyen Manja da ke masarautar Chakfem a Mangu da kuma kauyen Tangur da ke Bokkos.
Bayanai sun nuna maharan sun farmaki yankunan ne a lokuta daban-daban.
- 2027: ‘Sai bayan babban taron APC Tinubu zai bayyana wanda za su yi takara tare’
- Za mu iya galaba kan Iran ko babu Amurka — Isra’ila
Yayin da aka kai harin Tangur wajen misalin karfe 9:00 na dare, shi kuma na Manja an kai shi ne tun da gefen almuru.
Majiyoyi daga yankunan sun ce maharan sun bude wuta suka karkashe mutanen kafin daga bisani su cika wandunansu da iska.
A cewar majiyoyin, an kashe mutum bakwai a Mangu, a Bokkos kuma mutum 10.
Sun kuma ce maharan, wadanda ke dauke da bindiga sun rika harbin kan mai uwa da wabi sannan suka rika haura gidajen mutane suna karkashe su.
Daraktan Al’adu na kungiyar Ci Gaban Mwaghavul, Shohotden Mathias Ibrahim, da kuma Daraktan da ke kula da sansanin ’yan gudun hijira na Mangu ne suka tabbatar da alkaluman mutuwar, inda suka ce yanzu haka ana zaman dardar a yankin.
Sai dai ya zuwa yanzu, shugabannin al’umma da kuma mazauna yankin ba su amsa sakon da wakiliyarmu ta tura musu na neman karinn bayani ba.
Kazalika, rundunar ’yan sandan jihar Filato ba ta magantu a kan hare-haren ba, sakamakon Kakakin runduna, Alfred Alabo, bai amsa kiran waya da sakon kar-ta-kwana da na Whatsapp din da wakiliyarmu ta tura masa ba, ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.