✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya bayar da umarnin binciken hare-haren Benuwe

Tinubu ya umarci gwamnan jihar da ya jagoranci yin sulhu tsakanin waɗanda rikicin ya shafa.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya umarci jami’an tsaro da su yi bincike tare da gano waɗanda suka kai hari a Jihar Benuwe, inda aka kashe sama da mutum 100.

Harin ya faru ne a ƙauyen Yelwata da ke Ƙaramar Hukumar Guma a jihar.

Bayan harin, matasa sun rufe hanyar Lafiya zuwa. Makurdi domin nuna ɓacin ransu.

Zanga-zangar ta ci gaba da gudana har zuwa safiyar ranar Lahadi a birnin Makurdi, babban birnin jihar.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zangar.

A daren ranar Lahadi, Shugaba Tinubu ya wallafa saƙo a a shafin sa na X, inda ya ce dole a kawo ƙarshen wannan kashe-kashe, kuma ya umarci jami’an tsaro su ɗauki mataki don kama duk masu hannu a rikicin.

Tinubu ya kuma buƙaci Gwamnan Jihar Benuwe, Hyacinth Alia, da ya jagoranci tattaunawa da yin sulhu tsakanin manoma da makiyaya domin wanzar da zaman lafiya.

Ya gargaɗi shugabannin siyasa da na al’umma da su guji furucin da ka iya haifar da tarzoma.

Ya ce lokaci ya yi da za a haɗa kai domin warware matsaloli da hanyar gaskiya, adalci da fahimta, domin a samu zaman lafiya a Jihar Benuwe.