✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe ’yan ɗaurin aure 12 daga Zariya a Filato

“Mun tsaya tambayar wasu mutane kwatance, kafin mu farga har sun yi mana ƙawanya sun zagaye motar ta kowace kusurwa, suna ihu cewa a kashe…

An yi wa wasu matafiya ɗaurin aure 12 kisan gilla bayan wasu mutane sun kai musu hari a yankin Mangu ta Jihar Filato.

Rahotanni sun bayyana cewa mutum 11 daga cikin matafiya suna samun kulawa a asibiti, bayan raunukan da suka samu a harin da aka kai musu a yankin Ƙaramar Hukumar Mangu a ranar Juma’a.

Aminiya ta samu labarin cewar an kai wa matafiya hari ne da misalin ƙarfe 8 na dare, a lokacin da su mutum 31, ciki har da mata da ƙananan yara, a cikin wata bas mallakin Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) ta Zariya.

Ayarin ’yan daurin auren da aka kai wa harin sun fito ne daga yankin Basawa da ke Zariya a Jihar Kaduna, lokacin da maharan suka tare su a kusa da yankin Ƙaramar Hukumar Qu’an Pan, suka kashe  mutum 12, ciki har da direban motar, wanda ma’aikacin jami’ar ne.

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), da ke Mangu, Sheikh Suleiman Haruna, ya tabbatar da faruwar lamarin, da cewa an ajiye gawarwakin a Babban Asibitin Mangu.

Sheikh Suleiman Haruna, ya ce, “Matafiya 31 ne a motar. Mun samu gawarwakin mutum takwas, amma mun roƙi jami’an tsaro su taimaka wajen kawo ragowar gawarwaki huɗu da suka rage.

“Muna tare da Shugaban Ƙaramar Hukumar Mangu kuma yana iya bakin ƙoƙarinsa a kan lamarin.”

Wani wanda ya tsallake rijiya da baya a harin, Ibrahim Umar, ya ce, “Mun kusa kaiwa Qu’an Pan bikin ɗaurin auren ɗan uwanmu, amma muka yi ɓatan kai saboda ba mu san hanyar ba.

“Mun tsaya tambayar wasu mutane kwatance, kafin mu farga har sun yi mana ƙawanya sun zagaye motar ta kowace kusurwa, suna ihu cewa a kashe mu, mu Hausawa ne.

“Daga nan suka fara duka suna kawo mana hari da muggan makamai. Direban suka fara kashewa kafin sauranmu, suka ƙona motar da gawarwakin mutane a ciki. Yanzu muna asibiti ana jinyar mu.”

Wakilimmu ya tuntuɓi kakakin ’yan sanda na Jihar Filato, DSP Alfred Altau, kuma jami’in ya shaida masa cewa yana sane da lamarin, amma sai nan gaba zai fitar da sanarwa a hukumance bayan tantance haƙiƙanin abin da ya faru.