Ana fargabar cewa ’yan bindiga sun kashe akalla mutum 100 a wani hari da suka kai a garin Yelewata da ke yankin Karamar Hukumar Guma a Jihar Benuwe.
Aminiya ta ruwaito cewa maharan sun far ma al’ummar garin na Yelewata ne a cikin daren ranar Juma’a wayewar garin Asabar.
- Wutar lantarki ta kashe mutum 5, ta jikkata 13 a Gombe
- Damina: NiMet ta gargaɗi jihohi 13 kan barazanar ambaliyar ruwa
Wadanda suka shaida harin na Yelewata sun ce maharan sun mamayi garin ne kafin karfe 12 na dare, inda suka kwashe sama da sa’a biyu suna ta’annati ba tare da wani dauki daga jami’an tsaro ba.
Da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, wani mai magana da yawun fadar gwamnatin Benuwe, Tersoo Kula, ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa maharan sun kone gidaje da dama.
Sai dai ya ce jami’an gwamnati da suka kai ziyara yankin na Yelwata sun samu cewa wadanda aka kashe ba su wuce mutum 45 ba.
Shi ma mai magana da yawun ’yan sandan jihar, Udeme Edet, ya ce jami’ansu sun yi musayar wuta da maharan.
Haka kuma, an wani harin na daban da ya auku an kashe sojoji biyu a garin Daudu, shi ma a yankin karamar hukumar ta Guma.
Wannan harin shi ne na uku a baya-bayan nan a garin Yelewata wanda ke kan iyakar jihar ta Benuwe da Nasarawa a cikin mako daya.
Ana iya tuna cewa a watan da ya gabata ne wasu mahara da ake zargin makiyaya ne suka kashe kimanin mutum 20 a karamar hukumar Gwer ta Yamma a jihar ta Benuwe.
Kungiyar Amnesty mai fafutikar kare hakkin dan Adam ta yi kira ga gwamnatin da ta dauki matakin dakile zubar jini da salwantar rayukan al’umma a kasar.
Amnesty ta ce gazawar gwamnatin Nijeriyar ce ta sanya asarar rayukan al’ummar kasar ta zama ruwan dare.